Lardin Jiangsu da ke tsakiyar kasar Sin ya yi suna ne saboda an samu koguna da tabkuna da yawa a nan, ya kuma shahara ne domin an fi samun tsoffin garuruwa a wajen. Garin Luzhi ya zama kan gaba a cikin dukkan tsoffin garuruwa da aka fi samun koguna saboda tarihinsa ya kai misalin shekaru 2500.
Garin Luzhi na cikin birnin Suzhou na lardin Jiangsu, fadinsa ya kai fiye da murabba'in kilomita 1 kawai. A bakin kofarsa ta yamma, bayan da masu yawon shakatawa suka wuce wani babban allon dutse da aka rutuba 'tsohon garin Luzhi' a kansa, sun kuma ketare gadar Luzhi, sun iya gamuwa da alamar garin Luzhi, wato wata dabba mai suna Lu Duan, wanda ke da kaho daya kawai. Akwai almarar cewa, sigogin musamman 2 da Lu Duan ke da su su ne da farko, ya iya gudu cikin sauri. Na biyu kuma, ya iya tattara labaru da yawa kuma cikin sauri. Sa'an nan kuma, Lu Duan ya iya yaren wurare daban daban, shi ya sa mazaunan wurin sun mayar da shi tamkar dabba mai kawo kwanciyar hankali. Malama Wang Yan, wadda ke jagorancin masu yawon shakatawa, ta yi bayani kan garinta na Luzhi cewa, 'An fara gina wannan tsohon gari ne a zamanin daular Chunqiu da Zhanguo na kasar Sin, wato yau da shekaru misalin dubu 2 da dari 5 da suka wuce. Kayayyakin gargajiya da aka tono a kudancin garin sun tabbatar da cewa, mutane sun fara rayuwa a nan yau da shekaru misalin 5500 da suka wuce, shi ya sa garinmu na da dogon tarihi ainun. Yanzu ya kasance da wani kogi da tituna 2 a nan. Tarihin gidajen da ke gabobin kogin ya wuce shekaru dari 1, inda ake sayar da abubuwa a bangare na gaba, mutane suna zama a bangare na baya ko kuma na sama. '
In kuna yawo a tsoffin tituna da gidaje da unguwoyi a Luzhi, to, kuna iya ganin sigogin musamman irin na gargajiya a ko ina. Yanzu akwai manyan tituna 9 a nan, inda aka gina yawancin gine-gine a kansu yau da shekaru dari 3 zuwa dari 4 da suka shige. An shimfida wadannan tituna da duwatsu na Cobble da Granite a gabobin kogin, shi ya sa mazaunan wurin suka dogara da kwale-kwale domin kaiwa da kawowa. A gabobin titunan akwai shaguna da yawa, kasuwa na ci sosai, masu yawon shakatawa na ta kaiwa da kawowa. Luzhi ya sha bamban da saura saboda an gina hanyoyin ruwa da yawa a nan, kuma yana kasancewa da dimbin ruwa da gadoji a wajen. Madam Liu Limei ta kai ziyara a Luzhi a karo na biyu daga garinta na birnin Xiamen, ta bayyana cewa, 'Tsohon garin nan na da al'adu masu dogon tarihi, ya kuma nuna sigar musamman ta wurin inda aka samu koguna da tabkuna da yawa. Masu yawon shakatawa suna iya yawo a nan cikin kwale-kwale, sa'an nan kuma, 'yan mata da ke sa tufafi irin na musamman suna tukin kwale-kwale da gorori, suna rera wakoki, wannan na da ban sha'awa sosai.'
Luzhi ya dade kuma ya sharaha ne a matsayin birnin gadoji a kudacin kasar Sin. A cikin gari mai fadin murabba'in kilomita 1 akwai gadojin dutse 72 da aka gina a dauloli daban daban na kasar Sin. A idanun masu yawon shakatawa da yawa, ziyarar Luzhi ta yi kama da ziyarar wani dakin nune-nunen gadojin gargajiya.
1 2
|