Ran 1 ga watan Agusta na wannan shekara rana ce ta cikon shekaru 80 da kafuwar rundunar 'yantar da jama'ar kasar Sin. A shekarun baya da suka wuce, saboda kasar Sin ta yi ta kyautata karfinta, shi ya sa ta kara hada gwiwa da kasashen duniya a fannin aikin soja. Tun daga shekarar 2000 har zuwa yanzu, kasar Sin ta sha shiga rawar daji ta aikin soja ko kuma ta musamman a tsakanin bangarori 2 da bangarori daban daban, sa'an nan kuma, ta kara bude kofarta a harkokin aikin soja a fili, ta yi musayar fasahohi da bangaren aikin soja na kasashen duniya domin himmantuwa wajen kiyaye zaman lafiyar duniya tare.
Bisa kididdigar da aka yi, an ce, yanzu kasar Sin ta kulla dangantakar hadin gwiwa tare da kasashe fiye da 150 ta fuskar aikin soja. Tun daga shekarar 1990, rundunar kasar Sin ta fara shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya. Tun daga shekarar 2000, kasar Sin ta sha gayyatar 'yan kallo na kasashen waje a fannin aikin soja ko kuma jami'ai masu kula da harkokin soja na ofisoshin jakadanci na kasashen waje a kasar Sin domin kallon rawar daji da sojojin Sin suka yi. Ban da wannan kuma, rundunar kasar Sin ta fara shiga wasu rawar daji a tsakanin bangarori 2 da bangarori daban daban.
Madam Yu Shujie, babbar kanar da ke aiki a cikin sashen nazarin harkokin soja na duniya na cibiyar nazarin ilmin soja ta rundunar 'yantar da jama'ar Sin, ta bayyana ra'ayinta kan wannan da cewa, makasudin kasar Sin a fannin yin hadin gwiwa da kasashen duniya a fannin aikin soja shi ne domin kara amincewa da juna ta fuskar aikin soja a tsakaninsu, da samar da kyakkyawan muhalli mai zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, da kuma daidaita barazana da kalubale daban daban ta fuskar tsaron kai tare. Ta ce,'Bayan da aka sa aya ga yakin cacar baki, halin da ake ciki a duniya ya sami manyan sauye-sauye, ana ta samun bunkasuwar tattalin arzikin duniya bai daya, haka kuma bangarori daban daban suna shiga cikin harkokin siyasa na duniya. A sa'i daya kuma, 'yan ta'adda da 'yan a-ware da masu tsattsauran ra'ayi da 'yan fashi a kan teku da masu laifuffuka a ketaren kasashe suna kasancewa tamkar barazana ga dukkan kasashen duniya a fannin tsaron kai. Don kiyaye zaman lafiya na duniya da kyautata tsaron kai tare da kuma samar da kyakkyawan yanayi a duniya, wajibi ne sojojin kasashen duniya su gama kansu domin daidaita barazanar da dan Adam ke fuskanta tare. A matsayinta na muhimmiyar kasa a duniya, kasar Sin tana da nauyi da kuma hakkin shiga wadannan ayyuka.'
Kwalejin ilmin harkokin tsaron kasa na jami'ar ilmin tsaron kasa ta rundunar 'yantar da jama'ar Sin na daya daga cikin sassan da rundunar Sin ta bude kofa ga kasashen duniya. A ko wace shekara, hafsoshi manya da matsakaita na kasashe da yawa sun zo nan don shiga kos na tsawon lokaci daban daban, inda malaman kasar Sin ba kawai suka yi bayani kan manufar kasar Sin a fannin tsaron kasa da tarihin rundunar Sin da tsarinta da ayyukan raya rundunar Sin ta zamani ba, har ma sun yi karin bayani kan al'adu da tarihin Sin da tsarinta na siyasa da na tattalin arziki da kuma manufofin Sin ta fuskar harkokin diplomasiyya da kabilu da addinai da dai sauransu.
Dadin dadawa kuma, a lokacin da suke karatu a nan, hafsoshin kasashen duniya sun iya kai ziyara ga sansanonin rundunar Sin, sun iya kallon makaman kasar Sin a kusa da su, sa'an nan kuma, sun sami damar shiga aikin horo da rawar daji na rundunar Sin. Suna ganin cewa, wannan ya shaida cewa, kasar Sin na kara bude kofarta a harkokin soja a fili. Kanar Rolando Moyano na rundunar kasar Argentina ya bayyana cewa,'A cikin watanni 4 da muke karatu a nan, mun ziyarci rundunar Sin, mun fahimci cewa, rundunar Sin tana da nagartacciyar fasaha, kuma ingancinta na da kyau. Ta bude kofarta ga kasashen duniya sosai. Mun iya fahimtar zaman rayuwar sojojin Sin daga fannoni daban daban. Ban da wannan kuma, ingancin rundunar Sin a fannonin hadin gwiwa da taimakawa juna na da kyau ainun.'
Kwararrun kasar Sin masu ilmin soja sun bayyana cewa, don kara hada gwiwa da kasashen duniya a fuskar aikin soja, nan gaba kasar Sin na bukatar ci gaba da yin shawarwari kan manyan tsare-tsare da yin tattaunawa kan harkokin tsaron kasa da yin hadin gwiwa a tsakanin bangarori daban daban da kuma rawar daji cikin hadin gwiwa da kuma horar da ma'aikata tare da kasashen duniya. Bayan wannan kuma, za ta kara yin mu'amala da hadin gwiwa da kasashen duniya a fannonin yaki da ta'addanci da ba da agaji domin bala'i da kare zaman lafiya da tabbatar da tsaron kai a kan teku da dai sauransu, za ta kara samun amincewa da juna tare da kasashen duniya. Sa'an nan kuma, za ta zabura wajen zaman lafiya da bunkasuwar yankin Asiya da tekun Pacific, za ta kuma ba da sabuwar gudummowa wajen raya duniya mai zaman lafiya da wadata tare da kuma jituwa cikin dogon lokaci.(Tasallah)
|