Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-09 17:07:39    
Wasu labaru game da jihar Tibet mai cin gashin kanta

cri

Bisa kididdigar da ma'aikatar harkokin hanyar dogo ta kasar Sin ta yi, an ce, yawan fasinjojin da aka yi sufurinsu ta hanyar dogo ta Qinghai-Tibet ya kai fiye da miliyan 1.3

Hanyar dogo ta Qinghai-Tibet hanyar dogo ce da ta fi tsawo, kuma ya fi tsayi daga leburin teku daga cikin hanyoyin dogo da suke tuddai a duk fadin kasashen duniya. A cikin shekara daya da ta wuce bayan kaddamar da wannan hanyar dogo, injuna da ma'aikatai da fasahohin yin amfani da ita sun ci jarrabawa iri iri da sauye-sauyen yanayi suka yi musu. Har yanzu ba a gamu da hadarurukan zirga-zirgar jiragen kasa, kuma ma'aikatai da fasinjoji suna koshin lafiya. Bugu da kari kuma, saurin jiragen kasa da ke tafiya a kan wannan hanyar dogo ta Qinghai-Tibet ya kai kilomita dari 1 a kowace awa.

Wani labari daban shi ne gwamnatin tsakiya da sauran wurare na kasar Sin suna taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da jihar Tibet gaba.

Bayan da kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da majalisar gudanarwa ta kasar Sin suka kira taron tattaunawa kan harkokin Tibet a karo na 3 a shekarar 1994, yawan kudin taimako da wurare daban-daban na duk kasar Sin suka samar wa jihar Tibet ya riga ya kai kudin Renminbi yuan biliyan 6.4. Wadannan kudade sun kafa wani tushe mai inganci wajen neman bunkasuwar jihar Tibet.

Wakilin kamfanin dillancin labaru na Xin Hua na kasar Sin ya samu wannan labari a gun taron aiki da aka yi a ran 28 ga watan Yuni a birnin Lhasa, babban birnin jihar Tibet.

Mr. Hao Peng, mataimakin zaunannen shugaban gwamnatin jihar Tibet mai cin gashin kanta yana ganin cewa, taimakon da gwamnatin tsakiya da jama'ar duk kasar Sin suka samar wa jihar ya taka muhimmiyar rawa wajen canja halin da ake ciki a birane da kauyukan jihar Tibet da kyautata ingancin zaman rayuwar jama'ar kabilun Tibet da kuma kara saurin bude kofa da yin gyare-gyare a jihar Tibet.

Labarin karshe na yau shi ne ana kiyaye hanyar namun daji da ke ratsa hanyar dogo ta Qinghai Tibet.

A kwanan baya, wakilinmu ya samu labari daga ma'aikatar hanyar dogo ta kasar Sin cewa, kamfanin hanyar dogo ta Qinghai-Tibet ya gyara hanyoyi 33 domin namun daji wadanda suke ratsa hanyar dogo ta Qinghai-Tibet domin kiyaye wadannan namun daji da suke zama a wuraren da ke dab da hanyar dogo ta Qinghai-Tibet. A waje daya an kafa shinge da alamomi da na'urorin da ke nuna wa namun daji hanyar da ya kamata su bi. (Sanusi Chen)