Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-06 17:42:36    
Daliban jami'o'i suna fatan makomar Hong Kong za ta kara samun kyatatuwa

cri
Yanzu, a nan birnin Beijing, ana yin nunin ci gaba da Hong Kong ya samu tun bayan da aka komo da shi a karkashin mulkin kasar Sin a cikin shekaru 10 da suka wuce. Bayan da daliba da yawa na jami'o'in Beijing suka ziyarci nunin, sun bayyana cewa, nunin ya gwada misalai da yawa kan kyakkyawan sakamako da aka samu wajen aiwatar da "manufar kasa daya tsarin mulki iri biyu" a Hong Kong, an ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da wadatuwa a Hong Kong a cikin shekarun nan 10 da suka wuce.

Bayan Wang Zhimin, dalibar jami'ar koyon aikin masana'antu ta birnin Beijing ta ziyarci nunin, ta ce, "na jiku sosai da nunin, kasarmu ta komo da Hong Kong karkashin mulkinta daga bisani, bisa matsayina na Basiniya, nake takama da wannan"

Ko da yake bayan da aka komo da Hong Kong a karkashin mulkin kasar Sin a cikin shekaru 10 da suka wuce, Hong Kong ya gamu da kalubale da rikicin kudi na Asiya ya kawo masa, da bulluwar annobar cutar Sars daya bayan daya, amma Hong Kong bai koma baya ba, akasin haka ya kai matsayi na 11 a fannin cinikayya a duniya, ya zama kasuwar sayar da kudaden musaya mafi girma na 6 a duniya da kasuwar hada-hadar kudi mafi girma na 2 a nahiyar Asiya. Ina ra'ayin dalibai da suka ziyarci nunin a kan wannan?

Daliba Wang Zhimin tana lura da kyakkyawan sakamako da aka samu wajen aiwatar da manufar "kasa daya, tsarin mulki iri biyu" a Hong Kong. Da ta tabo magana a kan wannan, sai ta ce, "an aiwatar da manufar "kasa daya, tsarin mulki iri biyu" da kyau a Hong Kong, manufar na dacewa da halin da muke ciki, da kuma bunkasuwar Hong Kong."

Dalibi Wu Hao wanda ke karatu a shahararriyar jami'a mai suna "Qinghua" ya fahimci irin babban kokari da mazaunan Hong Kong ke yi. Ya ce, "mazaunan Hong Kong suna kokari sosai wajen yin ayyukansu, sa'an nan hukumar Hong Kong da gwamnatin kasar Sin sun nuna musu babban goyon baya a cikin shekaru 10 da aka komo da Hong Kong a karkashin mulkin kasar Sin."

Bayan da daliba Zhen Kaiyin wadda ta zo babban yankin kasar Sin daga Hong Kong ta ziyarci nunin, sai ta ce, babban taimako da jama'ar babban yankin kasar suka bai wa Hong Kong a lokacin yaduwar annobar cutar Sars ya shaku cikin zuciyarta sosai. Ta kara da cewa, "a ganina, taimakon allurar rigakafin cutar da kyalen rufe baki da babban yankin kasar Sin ya bai wa Hong Kong ya ishe mu, don haka ba wani abu ke iya tsortar da mu."

A cikin shekarun nan 10 da suka wuce, an kafa tsarin inganta huldar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin babban yankin kasar Sin da Hong Kong. Babban yankin ya amince da jama'arsa masu zaman kansu da su yi yawon shakatawa a Hong Kong, ya kuma nuna goyon baya ga manyan masana'antu na gwamnatin kasar Sin da su sayar da takardun hannayensu a kasuwar hada-hadar kudi ta Hong Kong. Kazalika a cikin shekarun nan da suka wuce, babban yankin kasar da Hong Kong sun hada guiwarsu a fannin aikin ba da ilmi, kamar musayar dalibai da kafa makarantu da yin ayyukan binciken kimiya cikin hadin guiwa da sauransu.

Ban da wadannan kuma, ta hanyar nunin, an gano cewa, a cikin shekarun nan 10 da suka wuce, tsohon tsarin zamantakewar al'umma da tattalin arziki da zaman rayuwar jama'a bai canja ba a Hong Kong. Sa'an nan kuma matsayinsa na cibiyar aikin kudi da cinikayya da zirga-zirgar jiragen sama da na ruwa bai canja ba. Yanzu kuma, mazaunan Hong Kong suna kara nuna amincewarsu ga mahaifiyarsu wato kasar Sin, sa'an nan an kara tabbatar da wadatuwa a Hong Kong. Duk dalibai da suka ziyarci nunin, suna fatan makomar Hong Kong za ta kara samun kyatatuwa.(Halilu)