Kwanakin baya ba da dadewa ba, wani jami'in kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya furta a nan Beijing, cewa yanzu ana gudanar da aikin kafa cikakken tsarin tsaro na taron wasannin Olympic lami-lafiya. Domin magance yiwuwar aukuwar matsalolin tsaro, kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing zai dauki karin matakai a fannin kirkiro tsarin tsaro na ayyukan gina filaye da dakunan wasannin Olympic, da karfafa ayyukan yaki da ta'addanci da yunkurin tashin boma-bomai da kuma na yin musanye-musanye da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa a game da ayyukan tsaro na taron wasannin Olympic na Beijing, ta yadda za a cimma makasudin " gudanar da taron wasannin Olympic" lami-lafiya.
An labarta, cewa an rigaya an samu sakamako na hakika wajen gudanar da ayyukan tsaro na taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008. Alal misali: an kafa hukumomin bada umurni na kungiya-kungiya da kuma tsarin gudanar da ayyuka; Ban da wannan kuma, an kaddamar da " Cikakken tsarin tsaro na taron wasannin Olympic" yayin da aka gayyaci kwararru don su gabatar da rahotannin shaidawa kan ayyukan tsaro na taron wasannin Olympic na Beijing.
Mr. Zhang Shuyuan, mataimakin babban sakataren kwamitin shirya tsaron wasannin Olympic na Beijing bugu da kari mataimakin ministan tsaro na kwamitin ya fadi, cewa kirkiro ingantaccen tsarin tsaro,wani muhimmin abun tabbaci ne da za a samu ga "gudanar da taron wasannin Olympic lami-lafiya". Ya kasance da bukatu iri daban-daban na tsaro bisa bambancin halayen musamman na kowane fili da kuma daki na yin gasanni. Abin farin ciki, shi ne an cimma bukatun a cikin yunkurin gina filaye da dakunan wasanni. An kuma mayar da matakan tsaro na dukkan filaye da dakunan wasanni a matsayin wani cikakken tsari bisa kulawar ma'aikatar tsaro ta kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing.
Mr. Zhang Shuyuan ya kuma furta, cewa " muna gudanar da aikin kirkiro tsarin tsaro ta fuskar kimiyya da fasaha tare da daukar matakan bada tabbaci ga harhada na'u'rorin fasaha da kuma na gina filaye da dakunan wasanni cikin lokaci daya. Lallai ba a taba samun irin wannan misali a sauran kasashe ba. Don haka ne dai, mun samu yabo daga kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa".
Sa'annan Mr. Zhang Shuyuan ya jaddadda, cewa ma'anar kalmomin " taron wasannin Olympic na zaman lafiya", ita ce tabbatar da samun kwanciyar hankali sosai lokacin da ake gudanar da taron wasannin Olympic, da samar da kyawawan hidimomi a fannin tsaro a kuma kirkiro muhallin jituwa mai dorewa na zamantakewar al'ummar kasa.
Yanzu ya kasance da dimbin abubuwa masu amfani a gida da waje, wadanda suke iya bada tabbaci ga gudanar da ayyukan tsaro na taron wasannin Olympic lami-lafiya, wato ke nan yanzu ya kasance da zaman karko a al'ummar kasar Sin, wadda take samun bunkasuwar tattalin arziki yayin da take rika kyautata matsayin zaman rayuwar jama'a; kana kuma kasashe masu abuta da ita da kuma kwamitocin wasannin Olympic masu tarin yawa dukansu suna goyon baya da kuma taimaka wa kasar Sin wajen gudanar da ayyukan share fage ga shirya gagarumin taron wasannin Olympic.
Amma duk da haka, wajibi ne a mai da hankali kan wasu boyayyun abubuwan hana ruwa gudu wajen gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008. Kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing zai kafa cikakken tsarin tsaro na zamani na taron wasannin, wanda zai hada da tsarin bada umurni ga zirga-zirga, da kungiyoyin tsaro masu kwarewa, da kyakkyawan shirin yin hadin gwiwa da musanye-musanye tsakanin kasa da kasa da kuma shirin bada tabbaci ga bada guzuri da dai sauran fannoni domin tinkarar batun kwanciyar hankali na muhallin halittu, da batun samun bayanai da albarkatu lami-lafiya, da batun yaki da 'yan ta'adda, batun haramta makaman yada cututtuka da annoba da kuma makaman nukiliya, da batun yaduwar ciwace-ciwace, da batun barkata laifuffuka tsakanin kasa da kasa, da batun fataucin miyagun kwayoyi da kuma batun bakin haure da dai sauran batutuwa.
Ban da wadannan kuma, cibiyar bada umurni ta taron wasannin Olympic ta Beijing ta bada kwangilar daukar gwanaye sama da 70 a fannin tsaro na gida da na ketare; ta kuma kulla huldodin hadin gwiwa tare da sassan 'yan sanda na kasashe fiye da 20 domin ingiza musanye-musanye a fannin samun bayanai da fasahohi.
Ana kyautata zaton, cewa za a kammala aikin kirkiro tsarin tsaro na taron wasannin Olympic na Beijing ne a karshen wannan shekara.( Sani Wang )
|