Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-05 16:11:51    
Kasar Sin za ta cika alkawarinta na ba da taimako ga kasashen Afrika(B)

cri

Firayim Minista na kasar Sin ya ci gaba da cewa a cikin shekaru kusan talatin da suka shige bayan da aka kawo sauyi a kasar Sin da bude kofa ga kasashen waje,kasar Sin ta samo kanta wata hanyar bunkasuwa wadda ta dace da halin da take ciki,tattalin arzikinta na rika samun bunkasuwa,karfinta na kara karuwa a dukkan fannoni kuma a bayyane,zaman jama'arta na yi ta kyautatuwa.An samu manyan sauye sauye mai ma'anar tarihi a harkar kudade ta kasar Sin,musamman cikin shekarun baya,kasar Sin ta samu babban cigaba wajen gyara tsare tsarenta na kudade.Bankuna da yawa na cinikayya na mallkar gwamnati sun kawo sauyi kan tsare tsarensu na mallakar hannayen jari har ma sun sami babbar nasara wajen tafiyar da harkokinsu bisa tsare tsaren bankuna na zamani,ingancin jarinsu na karuwa a fili.Ana ci gaba da yin gyare gyare ga tsare tsare na kasuwannin kudade.Tsare tsare masu muhimmanci da kasuwannin hada hadar kudade takardun kudi wato stockmarket a turance ke bi su kara inganta.An fara tafiyar da wani sabon tsarin canja kudi na tsakanin kudin Sin Renminbi da kudade na sauran kasashen duniya,an kuma gaggauta kawo sauyi ta yadda a samu ruwan kudi bisa canzawar kasuwanni.Kasar Sin ta dosawa gaba wajen bude kofofinta na kudade sannu a hankali,ta cika alkawarin da ta dauka yayin da aka shiga da ita cikin kungiyar cinikayya ta duniya,ta fadada fagagen harkokin kudade da da'irar tafiyar da harkoki ga kasashen waje,hukumomin kudade na kasashen ketare da suka zo kasar Sin da kafa sassansu da tafiyar da harkokin kudi da zuba jari ko saye hannayen jari da sayarwa sai kara yawa suke yi.An tsaurara matakan sa ido da kafa dokoki kan harkokin kudade.Domin biyan bukatun cigaban hadewar manufofin tattalin arziki na duniya da bukatun kasarmu na yin gyare gyare da bunkasuwa,za mu kara kawo sauyi ga harkokin kudade daga dukkan fannoni,da gaggauta sabunta tsare tsaren kudade,da gaggauta kafa ka'idojin kudade da tsare tsaren kudade na zamani,da sa kaimi ga harkar kudade da ta bude kofa ga kasashen ketare,da kafa cikakkun dokoki na game da harkokin kudade,da inganta da tsaurara matakan sa ido da magance hadarorin kudade,za mu yi kokarin neman samun dauwamamen cigaban harkokin kudade lami lafiya.

A halin da ake ciki a yanzu,yanayin tattalin arziki da kudade na kasar Sin ya yi kyau.Duk da haka da kawai matsaloli da suke kasancewa kamar su rashin balas na tsakanin kudin shiga da na kashewa na duniya ya kara tsananta,saurin karuwar ajiyar kudaden kasashen waje a bankunan kasar Sin da rarar kudajen musanya a kasuwanni.Muna nan muna daukar matakai a dukkan fannoni domin daidaita wadannan matsaloli.Mun kara kawo sauyi ga harkokin kudade da sarrafa da su,mu bi hanyoyi da dama da suka dace wajen samar da kudade da ba da rance.Haka kuma mu kara sanya kokari wajen inganta tsare tsaren tattalin arziki da habaka bukatun dake akwai na gida,da inganta tsare tsaren ciniki na shigi da fici da sanya kokarin neman samun balas tsakanin kudin shiga da kudin kashewa a duniya,da kara kyautata tsare tsaren kula da kudaden kasashen ketare da kasar Sin ta tanada a bankunanta,da kara ingatan tsarin samun kudin canzawa tsakanin kudin Sin Renminbi da kudade na sauran kasashen duniya ta yadda ka'idar kasuwanni ta samarwa bisa bukatun da ke akwai ta taka rawa.Mu kyautata tsare tsare na kula da ajiyar kudaden ketare da amfani da su,mu fadada hanyoyi na amfani da kudaden ketare da ake ajiya.Muna tattare da imani cewa za mu iya warware dukkan matsalolin dake akwai a fannin kudade yadda ya kamata,da kiyaye dauwamamen cigaban da aka samu a harkar kudade lami lafiya.Wannan ba ma kawai ya taimaka cigaban tattalin arzikin Sin da zamantakewarta,hatta ma ya amfanawa zamam darko na tattalin arziki da kudade na duniya.

Tare da saurin karuwar tattalin arziki da cinikayya na kasar Sin da Afrika,kasar Sin da kasashen Afrika sun kara hada kansu a dukkan fannoni da sassa.Kasar Sin ta dora muhimmanci kan hadin kanta da bankin raya Afrika da hukumomin raya kasa na bangarorin Afrika.Musamman bayan da ta shiga bankin raya Afrika a shekara ta 1985,da akwai kyakkyawar dangantakar hadin kai tsakaninta da Afrika a kullum.Hadin kan kasar Sin da Afrika wani kashi ne na hadin kan kasa da kasa.Gwamnatin Sin tana so ta cigaba da hada kanta da sauran kasashe da sukumomin kudade na duniya ciki har da bankin raya Afrika,ta yi kokari tare da su wajen bude wata kyakkyawar makoma ga Afrika da kafa wata duniya mai daumawamen lafiya da wadatuwa da sulhuntarwa!

Yanzu ina sanar da budewar taron shekara shekara na kwamitin kula da kungiyar bankin raya Afrika na shekara ta 2007,ina fatan taron nan na shekara zai samu cikakkiyar nasara.Na gode kowa da kowa!

Jama'a masu sauraro,wannan ya kawo karshen raguwar jawabin da firayim minista na kasar Sin Wen Jiabao ya yi a taron kwamitin kula da kungiyar bankin raya Afrika da aka gudana a birnin Shanghai na kasar Sin a watan Mayu na wannan shekara da muke ciki.

Jama'a masu sauraro,akwai sauran lokaci kadan,za mu dan gutsura muku wani bayani da wani kwarare na kasar Sin ya rubuta kan cewa Afrika da kasar Sin suna bukatar juna.

A cikin bayaninsa,wannan kwarare ya yi nuni da cewa kasar Sin tana da muhimmiyar moriya a nahiyar Afrika.Saurin cigaban dangantaka dake tsakanin Sin da Afrika sakamako ne maras makawa na ci gaban zumunci da hadin kai tsakanin Sin da Afrika cikin dogon lokaci.Dalilai kuwa su ne na farko kasar Sin da Afrika suna taimakon juna wajen harkokin siyasa.Afrika wata muhimmiyar kungiyar ce da bai kamata a yi biris da ita a cikin harkokin duniya,tana da matsayin musamman a cikin daukacin harkokin waje na kasar Sin.Tasowar kasar Sin ta zaman lafiya tana bukatar goyon baya daga kasashen Afrika.Kasar Sin babbar kasa ce a duniya,kuma kasa ce mai tasowa,wannan shi ne tushen siyasa na manufar harkokin waje ta kasar Sin,wani muhimmin abu ne da kasar Sin ta yi la'akari da shi wajen harkokin waje.Ko a da ko a yanzu ko ma a nan gaba kasashe matasa ciki har da kasashen Afrika su ne muhimman kawaye na kasar Sin.Idan a ce kasashe matasa su ne tushen harkokin waje na kasar Sin,to kuwa kasashen Afrika su ma tushe ne na harkokin waje na kasar Sin.Na biyu ci gaban tattalin arzikin kasar Sin na bukatar albarkatai daga duk duniyia ta hanyar kasuwanci.Afrika tana da albarkatai masu dimbin yawa,kasuwanninta na da girma,kuma wani muhimmin kashi ne na tsare tsarem kasar Sin na samun kasuwanni da albarkatai daga gida da waje.Na uku kasar Sin tana bukatar goyon baya daga kasashen Afrika wajen neman dinke mahaifa..A halin yanzu da akwai kasashe biyar kawai na Afrika da suka kulla huldar jakadanci da Taiwan,wadannan kasashe kasashe ne da 'yan aware na Taiwan suka samu dauren gindi a duniya.Hadin kan kasar Sin da kasashen Afrika sun dakile yunkurin neman balle Taiwan daga kasar Sin da yan aware na Taiwan suke yi a duniya.

Kasashen Afrika su ma suna bukatar kasar Sin.A cikin shekarun baya,kasashen Afrika da suka sa lura ga kasashen gabas ko kasar Sin sai kara yawa su ke.Ko taron koli na Beijing na tattaunawar hadin kan kasar Sin da Afrika da shugabannin kasashen Afrika suka halarta wadda aka gudana a birnin Beijing na kasar Sin a shekara ta 2006 da ziyarar shugaban kasar Sin Hu Jintao ya kai a kasashe takwas na Afrika wadda kafofin yada labarai na kasashen Afrika suka labarta,dukkansu sun bayyana fatan kasashen Afrika na kafa wata muhimmiyar dangantakar kawaye tsakaninsu da kasar Sin.Wani dalili kuwa shi ne kasashen Afrika suna so su koyi da fasahohin da kasar Sin ta samu wajen raya kasa.na biyu suna so su rage dogaronsu kan kasashen yamma wajen tattalin arziki.Na uku kasashe da yawa na Afrika suna so su kubutar da kansu daga kangin talauci da samu cigaban tattalin arziki ta hanyar hadin kai da kasar Sin wajen tattalin arziki da ciniki.Da akwai wani dalili daban na siyasa,wasu kasashen Afrika suna so su koyi da fasahohin kasar Sin wajen tafiyar da harkokin mulki.A farkon shekarun 1990,wasu kasashen Afrika sun bi sawun kasashen yamma wajen sanya yanayin demokradiya a kasashensu amma wannan bai dace da halin da kasashensu ke ciki ba,shi ya sa kasashen Afrika su yi koyi da sauran kasashen duniya wajen tafiyar da harkokin mulki,kasar Sin ta zama misalin koyo wajen samun zaman karko na siyasa da saurin cigaban tattalin arziki. Wajen harkokin diplomasiya,wasu kasashen Afrika suna so kasar Sin ta kara taka rawa a cikin harkokin dundiya da ta zama wata kungiyar da ta yi kunnen doki da kasashen yamma da sassauta matsin kaimi na siyasa da kasashen yamma suka yi musu ta hanyar karfafa dangantaka dake tsakaninsu da kasar Sin.(Ali)