Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-05 13:16:06    
Bush ya sake kare yakin Iraki

cri

An labarta, cewa yau Alhamis, shugaba Bush na kasar Amurka ya yi ikirarin cewa cimma nasara a yakin Iraki na bukatar karin hukuri da karfin zuciya da kuma sadaukarwa. Wasu manazarta sun yi hasashen cewa, a gabannin bikin taya murnar samun mulkin kan kasar Amurka, Mr. Bush ya yi kira ga Amerikawa da su nuna goyon baya ga yakin Iraki da kara yi sadaukarwa, wannan dai ya shaida, cewa a halin yanzu gwamnatin Bush na fuskantar babban matsin lamba daga cikin kasar a kan batun Iraki.

Yau, Mr. Bush ya yi jawabin, cewa komai wahalhalun da za a samu a yakin Iraki, lallai kasar Amurka za ta cimma nasara. Ya kuma yi kira ga jama'ar kasar Amurka da su nuna goyon baya ga yakin da sojojin Amurka dake girke a Iraki da kuma gwamnatin Iraki suke yi don murkushe 'yan ta'adda ; Sa'annan ya sake jaddada, cewa kudurin tayar da yaki a Iraki da kuma na aike da karin sojoji zuwa Iraki yana da gaskiya kuma yana da muhimmancin gaske ga kasar Amurka.

Ko da yake Mr. Bush ya sha neman goyon gaya daga jama'ar kasar Amurka a kan batun Iraki, amma hakikanin abun da ya sa bata ransa shi ne Amerikawa mafi yawa sun nuna bacin rai ga makomar yakin Iraki. Wani sakamkaon binciken da aka samu ya yi nuni da, cewa yawan magoya bayan yaki Iraki a kasar Amurka ya sake ragu zuwa wani matsayi mafi kankanta, wato ke nan ya kai kashi 30 kawai cikin kashi 100. Yakin Iraki da ya ki ci ya ki cinyewa ya janyo hasarar rayukan sojojin Amurka kuma yanzu ana ta tashe-tashen hankula a kasar Iraki, duk wadannan sun sa mutane mafi yawan gaske na Amurka suka nuna rashin jin dadi ga gwamnatin Bush yayin da suke zargin manufar da take aiwatarwa a Iraki.

Wadanda suka fi yin Allah wadai da gwamnatin Bush a kan batun yakin Iraki su ne wadancan 'yan takarar shugabancin kasar Amurka daga Jam'iyyar Demokuradiyya. Madam Hillary Clinton daya daga cikinsu ta fadi a fili cewa, yakin Iraki ' yakin Bush' ne a zahiri. ' Saboda haka', in ji ta, ' wajibi ne Bush ya dauki alhakin lamarin saboda ya tayar da yaki da kuma ya ki kawo karshen yakin'.

Ban da wannan kuma, Mr. Barack Obama, dan majalisar wakilai daga jihar Illinois shi ma ya furta, cewa tun farko bai kamata majalisun dokokin kasar Amurka su danka wa shugaban kasar iznin afka wa kasar Iraki da yaki ba domin matakin soja da kasar Amurka ta dauka a Iraki ya zama tamkar wani sabuwar 'yanar gizo' mai daukar 'yan ta'adda da Amurka ta kafa a hakika domin kungiyar ' Al-Qaeda', wadda ta rigaya ta aike da 'yan ta'adda zuwa yankin Gabas ta Tsakiya da kuma sauran kasashe. Kazalika, tsohon dan majalisar wakilai Mr. John Edwards ya fadi cewa, yakin yaki da ta'addanci da gwamnatin Bush ya tayar, a zahiri dai, wani irin ' kirarin siyasa' ne, wanda ya zama abun fakewa ga Mr. Bush wajen tayar da yaki a Iraki.

Tare da kusantowar ranar babban zaben shugaban kasar Amurka da za a yi a shekara mai zuwa, dukannin 'yan takarar shugabancin kasar da kyar za su guje wa batun yakin Iraki. Domin samun karin goyon baya daga bainal jama'a, wadancan 'yan takara daga Jam'iyyar Republic su ma sun sha raba kawunansu da gwamnatin Bush. Yanzu, gwamnatin Bush ta fi yin bikin ciki ne domin wasu tsayayyun magoya bayanta sun riga sun canza matsayin da suka dauka kan yakin Iraki. Lallai wannan ya bakanta ran Mr. Bush. Mr. Richard Lugar,shahararren dan majalisar wakilai daga Jam'iyyar Republic bugu da kari wani kwararre a fannin harkokin waje ya bada lacca a gaban jama'a, inda ya yi kira ga gwamnatin Bush da ta sauya manufar da take aiwatarwa game da harkokin Iraki da kuma janye sojoji daga kasar tun da wuri. Sa'annan Mr. Lugar ya bukaci gwamnatin Bush da ta yi hadin gwiwa tare da majalisun dokokin kasar domin tattauna yadda za a sauya manufar da take aiwatarwa game da kasar Iraki. A karshe dai, Mr. Lugar ya yi kashedin, cewa idan ba a yi shiri tun da wuri ba, to wata rana kasar Amurka za ta ga tilas ne ta janye sojojinta cikin gaggawa.

Kafofin yada labaru na kasar Amurka sun yi hasashen cewa, wasu 'yan majalisa daga jam'iyyar Republic sun canza matsayin da suka dauka na goyon bayan yakin Iraki, wannan dai ya shaida, cewa lallai ana mayar da Mr. Bush a saniyar ware. ( Sani Wang )