Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-04 15:07:44    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(28/06-04/07)

cri
Ran 30 ga watan Yuni, an sa aya ga aiki na mataki na farko na sayar da tikitin shiga taron wasannin Olympic na Beijing. Bisa kwarya-kwaryar kididdigar da aka yi, an ce, yanzu kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing wato BOCOG ya karbi takardun neman samun tikiti fiye da dubu dari 7, yawan tikitocin da aka nemi samuwa ya wuce miliyan 4.9. Saboda yawan tikitocin shiga bikin bude da rufe taron wasannin Olympic da wasu gasannin da ke jawo hankulan mutane da aka nemi samuwa ya fi wadanda ake sayarwa ga jama'a yawa sosai, shi ya sa ana bukatar kada kuri'a domin tabbatar da mutanen da suka sami damar samun wadannan tikitoci.

A kwanan baya, a kasar Guatemala, darektan gudanarwa Gilbert Felli na kwamitin wasan Olympic na kasa da kasa wato IOC ya bayyana cewa, kwamitin IOC ya nuna gamsuwa kan ayyukan da kwamitin BOCOG yake yi. Mr. Felli ya kawo wa Beijing ziyara yau da makonni 2 da suka wuce, inda shi da sauran jami'an IOC suka ga kyakkyawan sakamakon da kwamitin BOCOG ya samu a ayyukan share fage ga taron wasannin Olympic na Beijing a idanunsu tare.

Ran 26 ga watan Yuni, an bude taron nune-nunen harkokin bai wa juna wutar yola ta taron wasannin Olympic na Beijing da cibiyar harkokin bai wa juna wutar yola ta kwamitin BOCOG ta shirya. Za a rufe wannan taro a ran 3 ga wata, inda ta hanyar nuna hotuna da samfurorin hakikanan kayayyaki ne ake yi wa 'yan kallo karin bayani kan ilmomi game da fasalolin da aka tsara kan wutar yola da aka samar da su domin taron wasannin Olympic na da da kuma hanyoyin bai wa juna wutar yola. Za a yi irin wannan taron nune-nune a larduna da jihohi masu tafiyar da harkoki da kansu da biranen da ke karkashin shugabancin gwamnatin Sin kai tsaye na kasar Sin kuma da wasu biranen ketare da za a yi aikin bai wa juna wutar yola daya bayan daya.

Ran 1 ga wata, a gun gasar wasan kwallon kafa ta mata ta duniya da aka yi bisa gayyata a birnin Qinhuangdao na kasar Sin, kungiyar kasar Sin ta lashe kungiyar kasar Thailand da ci hudu ba ko daya. Bayan wannan gasa, kungiyoyin kasashen Sin da Thailand da Mexico da kuma Italiya da ke shiga gasar za su je birnin Shenyang domin ci gaba da gasa ta zagaye na 2. (Tasallah)