Ranar 1 ga watan Yuli na shekarar da muke ciki, rana ce ta tunawa da cikon shekaru 10 da Sin ta maido da mulkinta a Hongkong, haka kuma rana ce ta cikon shekaru 10 da kafuwar yankin musamman na Hongkong. A cikin shekarun 10 da suka wuce, an aiwatar da manufar "kasa daya amma tsarin mulki iri biyu" da kuma manufar "mutanen Hongkong su da kansu ne ke gudanar da harkokinsu" a Hongkong yadda ya kamata, Hongkong ta tabbatar da albarka da kwanciyar hankali, a game da wannan, kafofin yada labarau na kasashen Jamus da Indiya da Japan da Koriya ta kudu da Birtaniya da dai sauransu sun nuna yabo sosai.
Jiya gidan rediyon muryar Jamus ya bayar da sharhin cewa, a lokacin da Birtaniya ta mayar da mulkin Hongkong a hannun kasar Sin a shekaru 10 da suka wuce, ba a rasa samun hasashe kan mummunar makomar Hongkong ba, amma duk da haka, akasarin wadannan hasashe ba su zama abin gaskiya ba. Bayan da Sin ta maido da mulkinta a Hongkong, Hongkong ba ta rasa matsayinta na cibiyar kudi ba, kuma mutanen Hongkong na ci gaba da samun 'yancin fadi albarkacin bakunansu. Ban da wannan, gwamnatin kasar Sin ta kuma cika alkawarinta na rashin sauya tsarin zaman al'ummar Hongkong cikin tsawon shekaru 50.
Sai kuma jaridar "Berlin Daily" ta ce, a karkashin jagorancin gwamnatin kasar Sin da kuma hukumar yankin musamman na Hongkong, an ci gaba da tabbatar da albarkar tattalin arzikin Hongkong. A shekarar 2006, yawan GDP da kowane mutumin Hongkong ya samu ya kai dallar Amurka dubu 38, wanda har ya kai wani sabon matsayi a tarihi. Idan an ce, Shanghai cibiyar kudi ce ta babban yankin kasar Sin, to, ma iya cewa, kasancewar Hongkong ginshikin da ke tsakanin Sin da kasashen waje a fannonin kudi da ciniki.
Bayan haka, jaridar Hindu ta bayar da rahoto a ran 1 ga wata cewa, a karkashin tsarin "kasa daya amma tsarin mulki iri biyu", yanzu jama'ar Hongkong suna ta kara sa hannunsu cikin harkokin siyasa, ana kuma ci gaba da gudanar da gyare-gyaren siyasa a Hongkong, bayan haka, cigaban tattalin arzikin Hongkong ma yana jawo hankulan jama'a sosai.
Akwai kuma jaridar "Mainichi Shinbun" ta Japan da ta bayar da sharhin edita a ran 1 ga wata da cewa, da ma a yayin da gwamnatin kasar Sin ke sanar da manufar "kasa daya amma tsarin mulki iri biyu", dimbin mazaunan Hongkong sun damu, amma ga shi yanzu shekaru 10 sun wuce, hankulansu ya kwanta, mutanen da suka kaura zuwa kasashen ketare ma sun koma Hongkong.
Sai kuma jaridar "Choson Ilbo" ta Koriya ta kudu ta buga wani bayani a jiya, wanda ke da lakabin "hirar da gwamnan yankin musamman na Hongkong: Hongkong na da kyakkyawar makoma". Bayanin ya ce, "A yayin da Mr.Donald Tsang, gwamnan yankin musamman na Hongkong ke yin hira da dan jarida, cike yake da alfahari ga nasarorin da Hongkong ya samu a cikin shekaru 10 da sake hadewarta da kasarta ta asali, kuma yana da imani sosai ga makomar Hongkong",
Har wa yau kuma, wani sharhin da jaridar "The Economist" ta kasar Birtaniya ta bayar a ranar 30 ga watan Yuni da ya wuce, ya yi nuni da cewa, Hongkong na iya ci gaba da tabbatar da hanyar zaman rayuwa ta musamman bayan hadewa da kasarta ta asali, ma iya cewa, wannan gwaji wanda ba a taba samun irinsa ba a tarihi ya cimma nasara. A cikin shekaru 10 da Sin ta maido da mulkinta a Hongkong, Hongkong ta fuskanci kalubale iri iri masu tsanani, ciki har da matsalar kudi ta Asiya da cutar Sars da cutar murar tsuntsaye da dai sauransu, amma Hongkong ta haye wahalolin, yanzu tattalin arziki Hongkong na cikin wani zamani mafi kyau yau da shekaru 20 da suka wuce.(Lubabatu)
|