Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-03 17:54:09    
An kafa tsarin jin kai a jihar Tibet

cri

Tun daga ran 1 ga watan Yuli, an soma aiwatar da ma'aunin zaman rayuwa mafi kankanta a kauyukan jihar Tibet. Sabo da haka, ya zuwa yanzu, an riga an kafa kwarya-kwaryar tsarin jin kai da ke bisa tushen tabbatar da zaman rayuwar jama'a da na samar da wurin kwana da jiyya da ilmi ga mazaunan jihar domin tabbatar da zaman rayuwar jama'ar jihar.

Bisa wannan tsari, gidan da yawan kudin shiga da kowane iyalansa bai kai kudin Renminbi yuan dari 8 a kowace shekara zai shiga wannan tsari. Sabo da haka, manoma da makiyaya dubu 230 wadanda suke fama da talauci sosai za su samu moriya daga wannan tsari.

Ya zuwa karshen shekarar 2006, yawan mazaunan biranen jihar da ake samar musu kayayyakin jin kai ya riga ya kimanin dubu 44. Ma'aunin zaman rayuwa mafi kankanta ya kai kudin Renminbi yuan 130 a kowane wata a shekarar 1997, amma yanzu wannan adadi ya riga ya kai kudin Renminbi yuan 230 a kowane wata.

Bugu da kari kuma, jihar Tibet tana kokarin kafa wani sabon tsarin jin kai da zai dace da bunkasuwar tattalin arziki da zaman rayuwa na jihar, kuma zai shafi dukkan mazaunan jihar, kuma zai shafi fannoni daban-daban. (Sanusi Chen)