Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-03 15:59:54    
Vitamin D ta iya fama da ciwon sankara

cri

Yanzu za mu soma gabatar muku da labarin da muka shirya muku. Rahoton daga cibiyar nazarin ciwon sankara ta kasar Faransa ya bayyana cewa, mai yiwuwa ne karancin vitamin D a cikin jikin dan Adam zai haddasa karuwar yawan kamuwa da ciwon sankara. Masu ilmin kimiyya sun shawarci mutane da su karfafa vitamin D ta hanyar shan hasken rana, ta yadda za a magance kamuwa da ciwon sankara.

Masu ilmin kimiyya na wannan cibiya sun yi bincike kan maza dubu 48 tun daga shekarar 1986 zuwa shekarar 2000. Sun yi nazari kan halin da jikunan mutane suke ciki wajen karbar vitamin D da kuma dukan sanadan jiki da na hankali da suka ba da tasiri kan mutane wajen shan hasken rana, kamar wani yana da kiba, ba ya son jin zafi, ko kuma ba ya son fatarsa ta canja zuwa baki da sai sauransu.

A karshe dai, sun gano cewa, idan wani mutum ya kara samun vitamin D da yawansa ta kai International Unit wato IU dubu daya da dari 5 a cikin jiki a ko wace rana, to, za a rage yawan yiwuwar kamuwa da ciwon sankara da kashi 17 cikin dari, yawan mutuwar masu fama da ciwon sankara zai ragu da kashi 29 cikin dari.

Sun kuma nuna cewa, vitamin D da yawanta ta kai International Unit wato IU dari 4 ta biyan bukatun mutune, wadda su kan samu ta hanyar cin abinci a ko wace rana, amma ta yi kadan ne sosai, in an kwatanta ta da wadda aka samu ta hanyar shan hasken rana a ko wace rana. A zarihi kuma, idan wani mai koshin lafiya a fatansa ya shan hasken rana har tsawon mintoci 30 a ko wace rana, to, za a samar da vitamin D da yawanta ta kai misalin International Unit wato IU dubu 20 a cikin jiki. Saboda haka, shan hasken rana babbar hanya ce da mutane suke bi wajen samun isasshen vitamin D, mai yiwuwa ne ya taka rawa wajen raguwar yawan kamuwa da ciwon sankara.

Saboda sakamakon da suka samu daga wajen yin nazari, masu ilmin kimiyya sun kara yin imanin cewa, vitamin D na iya fama da ciwon sankara. Amma sun tunatar da cewa, kada mutane su sha wasu magungunan vitamin D, shan magungunan vitamin D masu yawa yana kawo wa lafiyar mutane illa. Ban da wannan kuma, wajibi ne lokacin shan hasken rana ya dace da mutane.(Tasallah)