Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-03 11:40:11    
Hong Kong ta sami babban ci gaba a fannin ba da hidimomin jin dadin jama'a

cri

Ran 2 ga wata, shugaba Zhang Jianzong na sashen harkokin 'yan kwadago da jin dadin jama'a ta hukumar yankin musamman na Hong Kong ya bayyana cewa, bayan dawowar Hong Kong a karkashin shugabancin kasar Sin yau da shekaru 10 da suka wuce, Hong Kong ta sami babban ci gaba a fannin ba da hidimomin jin dadin al'umma a sakamakon kokarin da hukumar Hong Kong da rukunin jin dadin jama'a suke yi tare.

A gun bikin murnar ranar cikon shekaru 10 da dawowar Hong Kong a kasar Sin da rukunin jin dadin jama'ar Hong Kong ya shirya, Mr. Zhang ya yi karin bayanin cewa, tun daga shekarar 2006 zuwa ta 2007, hukumar Hong Kong ta kashe kudin Hong Kong da yawansa ya kai milisan biliyan 32.8 a harkokin jin dadin jama'a, ta kashe kudi mafi yawa a fannin nan ban da aikin ba da ilmi. Yawan kudade da hukumar Hong Kong ta kan kashe a zaman yau da kullum dangane da jin dadin al'umma ya karu da kashi 80 cikin kashi dari a cikin wadannan shekaru 10.

Mr. Zhang ya ci gaba da cewa, tun daga shekarar 1997 har zuwa yanzu, yawan kudaden taimako da sashen jin dadin al'umma ya bai wa hukumomi masu zaman kansu ya karu fiye da kashi 50 cikin kashi dari. Hukumar Hong Kong da hukumomi masu zaman kansu suna hada gwiwa kamar yadda ya kamata, ta haka hidimomin da abin ya shafa da suke bayarwa sun kara biyan bukatun mutane.(Tasallah)