A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, huldar da ke tsakanin Sin da Afirka tana ta samun karfafuwa, ana kuma kara yin hadin guiwa da mu'amala a tsakanin Sin da Afirka a fannin ilmi. A karshen shekarar 2005, gwamnatin kasar Sin ta kafa kwalejin Confucius a birnin Nairobi na kasar Kenya domin yada harshen Sinanci da al'adun kasar Sin. Wannan ce kwalejin Confucius ta farko da kasar Sin ta kafa a duk Afirka. A cikin wannan kwalejin Confucius, akwai wani malamin kasar Sin wanda ya yi shekaru 6 yana aiki a Afirka. A cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku wani bayani game da wannan malamin da ake kiransa Liu Yong.
Mr. Liu Yong, wani malami ne na jami'ar horar da malamai ta Tianjin. A shekarar 2001, ma'aikatar ilmi ta kasar Sin ta aika da shi zuwa kasar Tanzania domin koyar da ilmin injuna masu kwakwalwa a jami'ar kimiyya da fasaha ta Dares Salaam. Ya yi shekaru 5 yana aiki a kasar Tanzania. Sannan a farkon shekarar 2006, ya bar kasar Tanzania ya je kasar Kenya ya fara yin aiki a cikin wannan kwalejin Confucius na jami'ar Nairobi. Mr. Liu Yong ya ce,"Daliban Afirka suna da baiwa wajen koyon harshe. Lokacin da nake koyar musu harshen Sinanci, na ga suna mallaka da fahimta wannan harshe cikin sauri. Ba ma kawai suna mallakar abubuwan da nake koyar musu ba, har ma suna iya amfani da su cikin sauri. Sabo da haka, ina farin ciki sosai."
Mr. Liu Yong ya bayyana cewa, bayan kaddamar da kwalejin Confucius a jami'ar Nairobi, ka'idar da ake bi wajen koyar da harshen Sinanci ita ce, ana daukar hanyoyi daban-dabam wajen koyarwa. Mr. Liu Yong yana ganin cewa, ban da aikin koyar wa dalibai ilmi da ya kamata malamai su yi, abun da ya fi muhimmanci shi ne malamai da dalibai su kara yin musayar ra'ayoyinsu ta hanyoyi daban-daban. Mr. Liu ya ce,"Dangantakar da ke tsakanina da dalibai tana da kyau. Mu ba ma kawai malami da dalibai ba ne, har ma mu abokai ne. Na kan gayyace su da su zo gidana a karshen mako domin dafa musu abincin Sinawa, alal misali yin abincin Jiaozi. A ganina, gida aji na biyu a wasu lokuta."
Tsarin zaman rayuwa na Afirka yana shan bamban da na kasar Sin, game da wahalolin da yake sha a Afirka, Mr. Liu Yong ya ce,"Tsarin zaman rayuwa na Afirka yana koma da baya sosai idan an kwatanta shi da na kasar Sin. A wasu lokaci, ba a iya samun ruwa mai tsabta har na tsawon rabin wata, a wasu lokuta babu wutar lantarki har na tsawon wata daya. A kasar Sin, wannan ba zai iyuwa ba ne. Babu sanran hanya zan iya zaba, sai na kau da irin wannan matsala da kaina. Alal misali, idan babu wutar lantaki, sai na yi amfani da kyandir. Na kan ci abinci a karkashin hasken kyandir, wannan kuma abu ne na farin ciki."
A cikin shekaru 6 da suka wuce, malami Liu Yong ya riga ya saba da irin wannan zaman rayuwa a Afirka. Amma dalilin da ya sa ya fara sabawa da irin wannan zaman rayuwa a Afirka shi ne, a cikin Sinawa wadanda suke aiki da zama a Afirka, a kan fadi cewa, "kafin a zo Afirka, ana jin tsoron Afirka, amma bayan isowar wani mutum a Afirka, zai son Afirka. Bayan a tashi daga Afirka, za a tuna da Afirka". Kamar sauran mutane suke ciki, a lokacin da Liu Yong ya isa Afirka, ya kuma kamu da ciwon sauro, kuma domin shi kadai yana Afirka, ya kan tuna da iyalansa da ke kasar Sin, yana kuma son dawo nan kasar Sin. Amma sannu a hankali ne tunaninsa ya samu canzawa. Ya ce,"Sannu a hankali ne na fara kaunar Afirka. Jama'ar Afirka mutanen kirki ne masu faran-faran. Kuma sun fi son Sinawa. Sabo da haka, na soma kaunarsu sannu a hankali. Idan ba haka ba, shi ke nan, ban iya zama a Afirka har na tsawon shekaru 6 ba."
A cikin zuciyar dalibansa, Liu Yong wani nagartaccen malami da abokinsu ne. A waje daya, a idon abokansa na aiki, shi wani abokin aiki ne mai kyau. A cikin wadannan shekaru 6 da suka wuce, ya dawo gidansa a kasar Sin ba sau da yawa ba, a kowane karo, tsawon lokacin da ya zauna a gida bai kai wata daya ba. Lokacin da yake tabo magana kan iyayensa da abokiyarsa, malami Liu Yong ya ce ya kamata ya nuna musu godiya. "Iyalaina suna nuna mini goyon baya. Idan ina son yin wani abun da nake so, kuma zan iya samu sakamako mai kyau, wannan abu ne mai kyau. Sabo da haka, suna nuna mini goyon baya."
Malami Liu Yong ya ce, yana son ci gaba da yin aiki a Afirka.(Sanusi Chen)
|