Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-02 21:29:54    
Hong Kong da babban yankin kasar Sin suna nuna himma ga hadin kansu a fannin wasannin motsa jiki

cri
Bayan da aka komo da Hong Kong a karkashin mulkin kasar Sin a shekarar 1997, Hong Kong ya zama wani yankin musamman na kasar. A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, Hong Kong ya nuna himma ga yin ma'amala da hadin kai a tsakaninsa da babban yankin kasar Sin a fannin wasannin motsa jiki daidai kamar yadda yake yi a fannonin ba da ilmi da kiwon lafiya da aikin kudi da sauransu.

Yau da shekaru 10 ke nan da aka komo da Hong Kong a karkashin mulkin kasar Sin. A sakamakon bunkasuwa da aka samu a cikin shekarun nan 10 da suka wuce, Hong Kong ya sami ci gaba a fanoni daban daban wadanda suka hada da wasannin motsa jiki. Malam Timothy Fok shugaban yanzu na hukumar wasannin Olympic ta Hong Kong ne. Da ya tabo magana kan wasannin motsa jiki da aka yi a da da yanzu a Hong Kong, sai ya jiku sosai cewa, "kafin an komo da Hong Kong a cikin kasar Sin, mun kokarta wajen bunkasa wasannin motsa jiki na gargajiyar Birtaniya kamar wasan kurket da wasan kwallon dauki-ruga kawai. Amma bayan da aka komo da Hong Kong a cikin kasar Sin, muna bunkasa wasannin motsa jiki a fannoni daban daban, musamman ma mun sami ci gaba wajen bunkasa wasannin motsa jiki da babban yankin kasar Sin ya dade ya kware, wadanda suka hada da wasan kwallon tebur, da wasan badmindo. Sa'an nan kuma mun kara halartar gasanni masu yawa kamar wasan motsa jiki na duk kasar Sin da sauransu."

Hanyoyi da ake bi wajen yin ma'amalar wasan motsa jiki a tsakanin babban yankin kasar Sin da Hong Kong yana da dama. Daya daga cikinsu ita ce, a yi amfani da gine-ginen wasan motsa jiki na babban yankin kasar Sin wajen horar da 'yan wasa na Hong Kong cikin wani tsawon lokaci. Malam Peng Chong, babban sakatare mai aikin sa kai na hukumar wasannin Olympic ta Hong Kong ya bayyana taimako da babban yankin kasar Sin ya bai wa Hong Kong a fannoni daban daban. Ya ce, "muna horar da kungiyoyin 'yan wasan tsare keke da na wasan kwallon tebur da wasan badmindo na Hong Kong a babban yankin kasar Sin, dalilai biyu da suka sa haka su ne, babu tazara sosai a tsakanin Hong Kong da babban yankin kasar Sin, na biyu kuma kudin da ake kashewa wajen yin haka kadan ne. Ban da wadannan wasanni, tun daga shekarun 1950, mun riga mun fara aika da 'yan wasanmu zuwa babban yankin kasar Sin don horar da su a fannonin wasan guje-guje da tsalle-tsalle da ninkaya, kuma sun sha shiga gasar wasannin nan da aka shirya a babban yankin kasar. Kazalika babban yankin kasar ya riga ya kai matsayin duniya a fannonin wasan takobi da na harba kibau, don haka Hong Kong ma ya iya samun damar yin koyi da 'yan wasanni na babban yankin kasar."

A wani fanni daban, Hong Kong ya shigo da gwanayen 'yan wasa daga babban yankin kasar Sin don shiga gasannin kasa da kasa cikin wakiltar Hong Kong. Alal misali, yanzu, kungiyar 'yan wasan kwallon tebur ta Hong Kong tana da 'yan wasa Li Jing da Gao Lize wadanda ta shigo da su daga babban yankin kasar. Haka kuma bayan da kungiyar wasan badmindo ta Hong Kong ta shigo da gwanayen 'yan wasa mata Wang Chen da Zhou Mi daga babban yankin kasar, yanzu ta riga ta zama abokan karawa mai karfi ga 'yan wasa na kasar Sin a cikin gasar tsakanin mata zalla. Malam Chen Zhicai, babban malamin koyarwa na kungiyar wasan badmindo ta Hong Kong ya bayyana ra'ayinsa cewa, "a ganina, ana cin gajiyar yin haka sosai. 'Yan wasa na Hong Kong sun koyi abubuwa da yawa daga wajen wadannan gwanayen 'yan wasa na babban yankin kasar Sin ta hanyar yin horaswa tare. Sa'an nan 'yan wasa matasa na Hong Kong sun sami taimako daga wajensu don kara daga matsayinsu a fannin fasaha da dabaru da kwarin guiwa. "

Za a shirya wasannin Olympic na yanayin zafi na shekarar 2008 a birnin Beijing da sauran birane na kasar Sin wadanda suka hada da Hong Kong. Yanzu, bangaren wasan motsa jiki na Hong Kong yana mai da hankali sosai ga wasannin Olympic da za a shirya a Beijing musamman ma a Hong Kong. (Halilu)