Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-02 20:53:44    
A shekarar bana, yawan 'yan yawon shakatawa da Tibet za ta karba zai zarce miliyan 3

cri

Hukumar yawon shakatawa ta jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin tana kyautata zaton cewa, a shekarar 2007, yawan 'yan yawon shakatawa da Tibet za ta karba zai zarce miliyan 3.

Wani jami'in hukumar yawon shakatawa ta Tibet ya fadi cewa, tun bayan da aka soma aiki da hanyar dogo da ta hada Qinghai da Tibet a watan Yuli na shekarar 2006, an daidaita matsalar sadarwa game da bunkasuwar sha'anin yawon shakatawa a Tibet, sabo da haka ne an sa kaimi sosai ga bunkasuwar sha'anin yawon shakatawa a Tibet. Game da saurin karuwar 'yan yawon shakatawa, Tibet ta dauki matakai a jere domin 'yan yawon shakatawa su ji dadin ziyarce ziyarcensu.

Bisa kididdigar da aka bayar, an ce, a shekarar 2006, yawan 'yan yawon shakatawa daga gida da waje da Tibet ta karba ya zarce miliyan 2.5, kudin shiga da aka samu daga yawon shakatawa ya kai kusan kudin Sin Yuan biliyan 2.8, wanda ba a taba ganin irin yawansa ba a tarihi.(Danladi)