Yau jaridun Hongkong sun bayar da rahotanni sosai kan bukukuwa iri daban daban da aka gudanar don murnar cikon shekaru goma da Sin ta maido da mulkinta a Hongkong. Ana ganin cewa, tsayawa tsayin daka kan fannoni hudu da shugaba Hu Jintao ya gabatar na da muhimmiyar ma'ana ga cigaban harkar "kasa daya amma tsarin mulki biyu" a Hongkong a nan gaba.
Jaridar "Wenhui" ta ba da sharhin cewa, muhimmin jawabin da shugaba Hu Jintao ya gabatar a gun taron murnar cikon shekaru 10 da Sin ta maido da mulkinta a Hongkong ya takaita nasarori hudu da aka cimma wajen aiwatar da manufar "kasa daya amma tsarin mulki biyu" a Hongkong a shekaru 10 da suka wuce, wato na farko, ya kamata a tsaya tsayin daka a wajen fahimtar manufar "kasa daya amma tsarin mulki biyu" da kuma aiwatar da ita yadda ya kamata kuma daga dukan fannoni, sa'an nan, a tsaya tsayin daka a kan gudanar da harkoki daban daban bisa babbar dokar Hongkong sosai, na uku, a tsaya tsayin daka kan bunkasa tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar jama'a, na hudu a tsaya kan kiyaye kwanciyar hankalin zaman al'umma. Nasarorin hudu suna da muhimmiyar ma'ana ga cigaban harkar "kasa daya amma tsarin mulki biyu" a nan gaba.(Lubabatu)
|