Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-02 17:49:51    
Wasu labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri

A cikin shirinmu na yau, da farko dai za mu kawo muku wasu labaru game da jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin.

Labarin farko shi ne, ingancin muhallli na jihar Tibet yana cikin hali mai kyau.

A kwanan baya, gwamnatin jihar Tibet mai cin gashin kanta ta bayar da wata sanarwa game da halin muhalli ke ciki a jihar a shekarar 2006. Bisa wannan sanarwa, an ce, ingancin muhalli na jihar Tibet yana cikin hali mai kyau a shekarar da ta gabata, wato har yanzu jihar Tibet na daya daga cikin yankunan da ke da ingancin muhalli mafi kyau a duk fadin duniya.

Wannan sanarwa ta bayyana cewa, ingancin ruwa na yawancin muhimman koguna da tafkuna na jihar suna kuma cikin hali mai kyau a shekarar da ta gabata. A waje daya, mazaunan birnin Lhasa ma suna shakar iska mai inganci a kusan duk shekarar bara.

Sannan kuma bisa kididdigar da aka bayar, an ce, fadin filayen ciyayi na halitta da ke jihar Tibet ya kai hektoci fiye da miliyan 82 kamar a da, wato bai samu sauye-sauye ba. Bugu da kari kuma, an riga an kafa gandunan daji da albarkatun da ke cikinsu guda 38 da fadinsu ya kai murabba'in kilomita dubu dari 4, wato yana matsayin farko a duk fadin kasar Sin.

Wani labari daban shi ne, yawan masu yawon shakatawa da suka kai ziyara a jihar Tibet a cikin farkon watanni 5 na shekarar da muke ciki yana ta samun karuwa.

Bisa kididdigar da hukumar kula da harkokin yawon shakatawa ta jihar Tibet ta bayar, an ce, a cikin farkon watanni 5 na shekarar da muke ciki, yawan masu yawon shakatawa da suka kai ziyara a jihar ya kai dubu 670, wato ke nan ya karu da kashi 82 cikin kashi dari bisa na makamancin lokaci na shekarar 2006.

Tun daga watan Janairu zuwa watan Mayu na shekarar da muke ciki, yawan masu yawon shakatawa da suka zo daga yankunan Hong Kong da Macao da Taiwan na kasar Sin ya ninka sau biyu, yawan masu yawon shakatawa da suka zo daga kasashen waje ma ya samu karuwa fiye da kashi 60 cikin kashi dari bisa na makamancin lokaci na shekarar bara.

Wani jami'in hukumar yawon shakatawa ta jihar Tibet ya ce, bayan kaddamar da hanyar dogo ta Qinghai-Tibet a shekarar 2006, an riga an kawar da cikas da ke hana bunkasuwar sana'ar yawon shakatawa a jihar Tibet kwata kwata.(Sanusi Chen)