Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-02 14:10:19    
Dubban mutanen Hongkong suna ribibin kallon panda

cri

A ran 1 ga watan Yuli, panda biyu, wato Yingying da Lele da gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta samar wa yankin musamman na Hongkong a matsayin kyauta sun fara ganawa da masu yawon shakatawa a lambun shan iska na teku na Hongkong. Wani jami'in wannan lambun shan iska ya bayyana cewa, yawan mutanen da suka shiga lambun shan iska domin kallon wadannan panda biyu ya kai fiye da dubu 20.

Kafofin watsa labaru na Hongkong sun bayar da labari cewa, a wannan rana da sassafe ne mutanen Hongkong da masu yawon shakatawa da yawa suna isa lambun shan iska na teku na Hongkong domin neman izinin kallon wadannan panda biyu musamman. Kafin a bude kofar lambun shan iska, yawan mutanen da suke jira a gaban kofar ya riga ya kai kimanin dubu 5. Ba a taba ganin irin wannan al'amari a da a wannan lambun shan iska ba. Sabo da haka, hukumar lambun shan iska ta tsai da kudurin bude kofa ga masu yawon shakatawa kafin lokacin da aka tsaida.

A waje daya, Mr. Sheng Zhiwen, shugaban lambun shan iska na teku na Hongkong ya bayyana cewa, wadannan panda biyu, wato Yingying da Lele suna wasa ko cin abinci kamar yadda ya kamata, babu kowane hadari ya faru.(Sanusi Chen)