Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-02 14:26:00    
Ofishoshin jakadancin kasar Sin da ke wakilci a kasashen waje da sinawan da ke zama a kasashen waje sun yi murnar ranar cika shekaru goma da maido da Hongkong a karkashin mulkin kasar Sin

cri

Ofishoshin jakadancin kasar Sin da ke kasar Togo da Sweden da Singgapore da sinawan da ke zama a birnin New York na kasar Amurka da kasar Togo sun shirya shagulgula kwanan baya don murnar ranar cika shekaru goma da maido da Hongkong a karkashin mulkin kasar Sin.

A ranar 1 ga watan Yuli a birnin Lome, hedkwatar kasar Togo, sinawan da ke zama a birnin sun taru gu daya don yin matukar murnar ranar cika shekaru goma da maido da Hongkong a karkashin mulkin kasar mahaifa. Jakadan kasar Sin da ke wakilci a kasar Mr Yang Min ya halarci taron don yin murna , kuma ya yi jawabi, inda ya bayyana cewa, dalilin da ya sa Hongkong ya sami bunkasuwa lami lafiya tun daga ranar da aka maido da shi a karkashin mulkin kasar Sin har zuwa yanzu, da kuma sai kara kyau yake yi shi ne saboda na da nasaba da inganci da bunkasuwa da kasar mahaifa ta kara samuwa sosai, shugaban kungiyar sada zumunci ta sinawan da ke zama a kasar Togo ya bayyana cewa, a cikin shekaru goma da maido da Hongkong a karkahsin mulkin kasar Sin, Hongkong ya sami bunkasuwar tattalin arziki tare da zaman karko wajen siyasa. Manufar aiwatar da tsarin Sin daya tak a duniya tare da aiwatar da mulki iri biyu da kuma mutanen Hongkong su da kansu suke aiwatar da harkokin Hongkong da kuma aiwatar da harkokin Hongkong shi kansa sosai sun zama babban tabbaci ga samun wadatuwa da zaman karko a Hongkong, ya yi fatan Makomar Hongkong za ta kara kyau.

A ranar 30 ga watan Yuni, rukunin Sinanwan da ke zama a kasar Amurka sun shirya shagalin nuna wasannin fasaha don murnar ranar maido da Honkong a karkashin mulkin kasar Sin. Wakilin din din din na kasar Sin da ke wakilci a Majalisar Dinkin duniya Mr Wang Guangya da ke halartar shagalin, ya bayyana cewa, tsarin kasa daya tak a duniya tare da aiwatar da harkokin mulki iri biyu tare da nasara ya ba da jagoranci ga daidaita batun Taiwan, ya sa ran alheri ga farfado da al'ummar kasar Sin mai girma da cim ma babban buri na samun dinkuwar kasar mahaifa tun da wuri.(Halima)