Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-02 10:38:51    
Gamayyar kasa da kasa ta nuna babban yabo ga maido da Hongkong a karkashin mulkin kasar Sin cikin shekaru goma

cri
A ranar 1 ga watan Yuni, lokacin da ya cika shekaru goma da gwamnatin kasar Sin ta maido da Hongkong a karkashin mulkinta , gamayyar kasa da kasa sun nuna babban yabo ga sauye-sauyen da aka samu bisa sakamakon da gwamnatin kasar Sin ta maido da Hongkong a karkashin mulkinta.

A ranar 1 ga watan, sabon ministan harkokin waje na kasar Britaniya Mr David Miliband ya bayar da wata sanarwar nuna yabo, inda ya ce, Hongkong ya sami sakamakon da ya jawo hankulan mutane sosai a cikin shekaru goma da aka maido shi a karkashin mulkin kasar Sin, Hongkong yana daya daga cikin manyan birane masu girma sosai a karni na 21. Sanarwar ta bayyana cewa, Hongkong ya tabbatar da tsarin da yake aiwatarwa cewa, "Kasar Sin daya tak a duniya tare da aiwatar da mulki iri biyu", Hongkong yana nan yana tafiya zuwa makomarsa mafi kyau.

Jaridar da ake kira "Hindu" ta kasar Indiya ta bayar da labari a ran 1 ga wannan wata, ta bayyana cewa, a karkashin tsarin da ake aiwatarwa game da "kasa daya tare da aiwatar da mulki iri biyu, jama'ar Hongkong sai kara yawa suke yi wajen halartar harkokin siyasa, kuma ana nan ana yin gyare-gyare kan siyasa a Hongkong, bunkasuwar da aka samu wajen tattalin arzikin Hongkong ta jawo hankulan mutane sosai.

A ranar daya ga wannan wata kuma, jaridar da ake kira "Yomiuri Shinbunthe" ta kasar Japan ta bayar da wani bayani, inda ta bayyana cewa, tun daga ranar da aka maido da Hongkong a karkashin mulkin kasar Sin cikin shekaru goma da suka wuce har zuwa yanzu, ba ma kawai ya zama tasmaharar kasar Sin da ke tinkarar zuwa duniya ba, hatta ma ya dauki nauyin zama wurin gwajin da masana'antun kasar Sin take zuwa kasashen waje, tsarin "Kasar Sin daya tak a duniya tare da aiwatar da mulki iri biyu" shi ma ya sanya rayayyen karfi ga raya tattalin arzikin kasar Sin.

Jaridar da ake kira "Frankfuter Allgemeine Zeitung" ta kasar Jamus ta bayar da wani bayani a ranar 30 ga watan Yuni cewa, a cikin shekaru goma da aka maido da Hongkong a karkashin mulkin kasar Sin , Hongkong yana ci gaba da kasancewa cikin zaman wadatuwa da zaman karko, ba ma kawai ya sami yabo wajen muhallin tattalin arziki ba, hatta ma yana kasancewa cikin zaman rayuwar siyasa iri daban daban da yawa, kuma yana ci gaba da zama babban birnin da ke da rayayyen karfi sosai.(Halima)