Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-01 21:53:12    
An gudanar da gaggarumin taron murnar cikon shekaru 10 da Sin ta maido da mulkinta a Hongkong

cri
Yau ranar 1 ga wata a cibiyar taro ta Hongkong, an gudanar da gaggarumin taron murnar cikon shekaru 10 da Sin ta maido da mulkinta a Hongkong wanda kuma ya kasance bikin rantsar da sabuwar gwamnatin yankin musamman na Hongkong. Babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin kuma shugaban kasar Sin, Mr.Hu Jintao ya halarci bikin, kuma ya bayar da wani muhimmin jawabi.

A ranar 1 ga watan Yuli na shekarar 1997, gwamnatin kasar Sin ta maido da mulkinta a Hongkong, kuma a hukunce ne yankin musamman na Hongkong ya kafu. Yau da safe, da misalin karfe 9, an bude gaggarumin taron murnar cikon shekaru 10 da Sin ta maido da mulkinta a Hongkong. Da farko dai, Mr.Donald Tsang ya yi rantsuwar kama mukaminsa na gwamnan yankin musamman na Hongkong. Sa'an nan, 'yan majalisar yankin musamman na Hongkong sun yi rantsuwar kama mukamansu daya bayan daya.

Bayan haka, shugaban kasar Sin, Mr.Hu Jintao ya yi jawabin cewa, a cikin shekaru 10 da Sin ta maido da mulkinta a Hongkong, gwamnatin kasar Sin ta aiwatar da manufar "kasa daya amma tsarin mulki guda biyu" da kuma manufar "mutanen Hongkong su da kansu ne ke gudanar da harkokinsu" yadda ya kamata, ta kuma tafiyar da harkoki daban daban bisa babbar dokar Hongkong. A cikin shekarun 10, Hongkong ta sami babban cigaba a wajen harkoki daban daban, mu'amala da hadin gwiwar da ke tsakaninta da babban yankin kasar Sin ma sai dinga bunkasa suke yi, bayan haka, Hongkong ta kuma kara inganta mu'amalar da ke tsakaninta da kasashen waje. Ya ce,"Yau a Hongkong, an tabbatar da kwanciyar hankalin zaman al'umma, an kara samun albarkar tattalin arziki, kuma an kara yadada dimokuradiyya yadda ya kamata, jama'a suna jin dadin zamansu. Hakikanan abubuwa sun shaida mana cewa, manufar "kasa daya amma tsarin mulki guda biyu" daidai ne, jama'ar Hongkong suna da hikima kuma suna iya gudanar da harkokin Hongkong yadda ya kamata, kuma Sin babban magoyi bayan Hongkong ne a wajen samun albarka da kuma kwanciyar hankali."

Mr.Hu Jintao ya jaddada cewa, cikon shekaru 10 da Sin ta maido da mulkinta a Hongkong yana da muhimmiyar ma'ana ga harkar "kasa daya amma tsarin mulki guda biyu", ya ce," 'kasa daya amma tsarin mulki guda biyu' wata hadaddiyar manufa ce, 'kasa daya' na nufin cewa, kamata ya yi a kiyaye ikon da dokoki suka bai wa gwamnatin tsakiya, kuma a kiyaye mulkin kan kasa da dinkuwarta da kuma tsaronta, sa'an nan, 'tsarin mulki biyu' na nufin kamata ya yi a tabbatar da ikon yankin musamman na Hongkong na cin gashin kansa. Manufar 'kasa daya amma tsarin mulki guda biyu' ba za ta iya taka rawarta sosai ba, sai dai bayan da aka tabbatar da wadannan fannoni biyu, hakan nan kuma, za a iya kawo wa jama'ar Hongkong alheri a hakika."

Shugaba Hu Jintao ya kuma yi nuni da cewa, kamata ya yi gwamnatin tsakiya na kasar Sin da gwamnatin yankin musamman na Hongkong da kuma jama'ar Hongkong su yi kokari tare, don kara ciyar da harkar "kasa daya amma tsarin mulki guda biyu" gaba. Ya sake bayyana cewa,"gwamnatin tsakiya za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka a kan aiwatar da manufar "kasa daya amma tsarin mulki guda biyu" da kuma manufar "mutanen Hongkong su da kansu ne ke tafiyar da harkokinsu", kuma za ta tafiyar da harkoki daban daban bisa babbar dokar yankin musamman na Hongkong, za ta nuna cikakken goyon bayanta ga gwamnan yankin musamman na Hongkong da kuma gwamnatinsa, za ta mara wa Hongkong baya a wajen bunkasa tattalin arzikinta da kyautata zaman rayuwar jama'arta da kuma cigaban dimokuradiyyarta, sa'an nan za ta sa kaimi ga mu'amala da hadin gwiwar da ke tsakanin babban yankin kasar Sin da Hongkong a fannonin tattalin arziki da ilmi da kimiyya da fasaha da al'adu da kiwon lafiya da wasannin motsa jiki da dai sauransu, kuma za ta nuna goyon baya ga Hongkong da ta bunkasa huldar da ke tsakaninta da kasashen waje. Gaba daya ne manufar gwamnatin tsakiya a kan Hongkong ita ce, domin Hongkong da kyakkyawar makomarta da jama'arta da kuma kyakkyawar makomar jama'arta.(Lubabatu)