Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-01 21:48:13    
An shirya gagarumin taron murnar ranar cikon shekaru 10 da dawowar Hongkong a kasar Sin

cri

A ran 1 ga wata a cibiyar taro da nune nune na Hongkong, an shirya gagarumin taron murnar ranar cikon shekaru 10 da dawowar Hongkong a kasar Sin da kuma bikin kama aiki da gwamnati na karo na 3 na yankin musamman na Hongkong ta yi.

Babban sakataren kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin, shugaban kasar Sin kuma shugaban hukumar soji ta kwamitin tsakiya na Jam'iyyar kwaminis ta Sin Mr Hu Jintao ya halarci taron kuma ya bayar da wani jawabi, inda ya yaba wa manyan nasarorin da Hongkong ya samu a cikin shekaru 10 da dawowar Hongkong a kasar Sin.

A wannan rana kuma, gwamna na karo na 3 na yankin musamman na Hongkong Mr Donald Tsang da sauran manyan jami'ai sun yi rantsuwar kama aikinsu.

Bisa wani labari daban da muka samu, an ce, a ran 30 ga watan jiya da yamma, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya gana da wakilai da suka fito daga bangarori daban daban na Hongkong, kuma ya bayar da wani muhimmin jawabi.

A cikin jawabinsa, Mr Hu ya ce, tabbas ne Hongkong zai samu wata kyakkyawar makoma, 'yan uwan Hongkong sun kware wajen kula da harkokin Hongkong da kuma raya shi da kyau.(Danladi)