Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-01 20:01:43    
Ministan harkokin waje na kasar Ingila ya bayyana cewa, Hongkong na da makoma mai haske

cri
Yau 1 ga wata, sabon ministan harkokin waje na kasar Ingila David Miliband ya bayyana cewa, Hongkong ya samu sakamako mai kyau a cikon shekaru 10 da dawowar Hongkong a kasar Sin, an tabbatar da manufar kasa daya "tsarin mulki iri biyu" cikin nasara, Hongkong na da makoma mai haske.

Mr. Miliband ya yi wannan bayani ne a cikin wata sanarwar tunawa da cikon shekaru 10 da dawowar Hongkong a kasar Sin. A cikin wannan sanarwar da aka samu daga babban ofishin karamin jakada na kasar Ingila da ke Hongkong, Mr. Miliband ya ce, Hongkong ya riga ya zama wani fifitaccen birni a karni na 21. Hongkong na da kwararrun nagartattu masu himmar aiki, kazalika yana da karfi wajen bunkasuwar tattalin arziki, kafofin watsa labaru kuma suna da 'yancin watsa labaru, bugu da kari Hongkong na da tsarin gwamnati da tsarin dokoki masu adalci kuma a fili, sabo da haka, yana da makoma mai haske.

Mr. Miliband ya bayyana cewa, kasar Ingila na fata Hongkong zai samu ci gaba a shekaru 10 masu zuwa, kuma nan gaba, za a karfafa dangantakar abokantaka da ke tsakanin Ingila da Hongkong. (Bilkisu)