Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-01 18:37:15    
Ra'ayoyin bainal jama'a na Hongkong da Macao sun yaba wa nasarorin da Hongkong ya samu bayan dawowarsa cikin kasar Sin

cri

A ran 1 ga watan Yuli, manyan jaridu na Hongkong da Macao sun bayar da labarai da yawa game da aikace aikace da shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya yi da kuma kyakkyawan halin da ake ciki a Hongkong domin taya murnar ranar cikon shekaru 10 da dawowar Hongkong cikin mahaifiya ta kasar Sin. Ra'ayoyin Bainal jama'a na Hongkong da Macao suna ganin cewa, a cikin wadannan shekaru 10 da suka wuce, Hongkong da babban yankin kasar Sin sun samu manyan nasarori da yawa a kan tarihin farfado da al'ummar kasar Sin da tarihin duniya.

Jaridar Wenhui ta Hongkong ta buga wani bayanin edita cewa, a cikin shekaru 10 da suka gabata da dawowar Hongkong a kasar Sin, an gudanar da manufar 'kasa daya, tsarin mulki iri biyu' da 'mutanen Hongkong su tafiyar da harkokinsu da kansu' yadda ya kamata, ta haka an kiyaye zaman karko da albarka a Hongkong. Gwamnatin tsakiya kuma tana mayar da manufar 'kiyaye albarka da zaman karko a Hongkong cikin dogon lokaci' a matsayin wani sabon muhimmin abu ga harkokin mulki da take yi, ta yadda za a iya tabbatar da cewa, Hongkong zai gudanar da harkokinsa bisa tsatin dokokinsa.

Jaridar Takung da jaridar kasuwanci ta Hongkong da kuma jaridar Macao daily su ma sun bayar da labarai da yawa game da aikace aikacen da ake gudana domin taya murnar ranar cikon shekaru 10 da dawowar Hongkong a kasar Sin.(Danladi)