Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-30 22:07:38    
Jaridar People's Daily ta bayar da sharhi don taya murnar ranar cikon shekaru 10 da dawowar HongKong cikin mahaifa ta Sin

cri
Jaridar People's Daily ta kasar Sin wadda za a buga ta a gobe wato ran 1 ga watan Yuli ta bayar da sharhi don taya murnar ranar cikon shekaru 10 da dawowar HongKong cikin mahaifa ta kasar Sin.

Sharhin ya bayyana cewa, shekaru goma na dawowar HongKong cikin mahaifa ta kasar Sin shekaru goma ne da aka bin manufar "kasa daya amma tsari biyu", kuma su shekaru goma ne da mazaunan HongKong suka gudanar da harkokin shiyyar da kansu, haka kuma su shekaru goma ne da aka rika samun wadata da kwanciyar hankali a shiyyar. Hakikannan abubuwa sun shaida cewa, manufar "kasa daya amma tsari biyu" ta yi daidai.

Ban da wannan kuma sharhin ya nuna cewa, yanzu neman samun bunkasuwa da kwanciyar hankali da jituwa ya riga ya zama ra'ayi daya na zaman al'ummar shiyyar HongKong. Sabo da mutanen sassa daban daban na HongKong suna hadin kansu bisa ra'ayin kishin kasa, da kuma neman ra'ayi daga bambancin da ake da shi, shi ya sa dole ne za su iya samar da wata makoma mai kyau ga HongKong.(Kande Gao)