Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-30 21:53:18    
Gwamnatin tsakiya ta kasar Sin tana fatan yankunan musamman na Hong Kong da Macao za su gama kansu domin kara samun bunkasuwa

cri
Ran 30 ga wata, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya bayyana cewa, Macao da Hong Kong dukkansu yankunan musamman ne na kasar Sin, suna da abubuwan bai daya da yawa wajen aiwatar da manufar 'kasa daya, amma tsarin mulki 2', suna iya koyi da juna game da wasu kyakkyawan sakamakon da suka samu daga ayyukan zahiri. Cikin sahihanci ne gwamnatin tsakiya ta kasar Sin tana fatan wadannan yankunan musamman 2 za su hada gwiwarsu domin kara samun bunkasuwa.

Shugaba Hu ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake ganawa da Edmund Ho, gwamnan Macao da ke halartar bikin cikon shekaru 10 da dawowar Hong Kong a karkashin shugabancin kasar Sin a ran nan da yamma. Hu ya kara da cewa, bayan dawowar Macao a kasar Sin yau da shekaru 8 da suka wuce, kasar Sin ta ci nasara a fannin aiwatar manufar 'kasa daya, amma tsarin mulki 2'. Macao ta sami babbar nasara a dukkan ayyukan raya ta. Gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta amince da ayyukan da Mr. Ho da hukumar Macao suka yi a cikin wadannan shekaru.

A nasa bangaren kuma, Mr. Ho ya yi wa gwamnatin tsakiya ta kasar Sin godiya saboda kulawa da goyon baya da take bai wa Macao. Ya kuma bayyana cewa, hukumar Macao za ta fuskanci abubuwan nan gaba, za ta gudanar da dukkan ayyuka yadda ya kamata domin yin kokarin tabbatar da samun bunkasuwar tattalin arziki mai dorewa da kwanciyar hankali da jituwa a harkokin zaman al'umma a Macao cikin dogon lokaci.(Tasallah)