A ran 30 ga wata, shugaba Hu Jintao na kasar Sin wanda ke halartar bikin murnar cikon shekaru 10 da dawowar ikon mulkin Hongkong a kasar Sin ya bayyana cewa, hakikanan abubuwan da aka yi a Hongkong bayan dawowar ikon mulkin Hongkong a kasar Sin sun bayyana sosai, cewar manufar aiwatar da "tsari iri biyu a cikin kasa daya" tana da makoma mai haske.
Shugaba Hu ya fadi haka ne a gun liyafar dare da gwamnatin yankin musamman ta Hongkong ta shirya.
Mr. Hu ya kara da cewa, hakikanan abubuwan sun shaida cewa, tunanin aiwatar da "tsari iri biyu a cikin kasa daya" da marigayi Deng Xiaoping ya bayar bisa ilmin kimiyya, ba ma kawai shiri mafi kyau ne wajen daidaita matsalolin tarihi na Hongkong ba, har ma wani tsari ne mafi kyau wajen tabbatar da kwanciyar hankali da bunkasuwa a yankin musamman na Hongkong cikin dogon lokaci bayan dawowar ikon mulkinsa a kasar Sin. Aiwatar da "tsari iri biyu a cikin wata kasa" yana kawo tasiri mai kyau ga Hongkong da duk kasar Sin da masu zuba jari na kasashe daban-daban da kuma bunkasuwar tattalin arzikin shiyya-shiyya. (Sanusi Chen)
|