Bayan kaddamar da hanyar dogo ta Qinghai-Tibet yau da shekara 1 da ta shige, yawan masu bin addinin Bhudda wadanda suke zuwa jihar Tibet domin aikin hajji yana ta karuwa.
Bisa kididdigar da gwamnatin jihar Tibet mai cin gashin kanta ta yi, an bayyana cewa, a cikin fadar Potala da dakin Ibada na Luobulinka da na Dazhao wadanda suke birnin Lhasa kawai, yawan masu bin addinin Bhudda da suka yi aikin hajji a shekarar da ta gabata ya kai dubu 328, wato ya karu da dubu 62 bisa na shekarar 2005.
Yawancin wadannan masu aikin hajji sun je jihar Tibet ne ta hanyar dogo ta Qinghai-Tibet. A waje daya, wasu 'yan kabilar Tibet sun je dakin Ibada na Tarsi da ke lardin Qinghai ne ta hanyar dogo ta Qinghai-Tibet. (Sanusi Chen)
|