Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-30 18:46:02    
Kafofin watsa labaru na Hongkong ya yaba wa ayyuka iri iri da shugaba Hu Jintao na kasar Sin ke halarta a Hongkong

cri

Jaridun yankin musamman na Hongkong da aka wallafe su a ran 30 ga wata sun yaba wa ayyukan da shugaban kasar Sin Hu Jintao ya halarta a ran 29 ga wata domin taya murnar cikon shekaru 10 da dawowar ikon mulkin Hongkong a kasar Sin. Suna ganin cewa, ayyukan da shugaba Hu ya halarta da jawabin da ya yi a kwana na farko bayan da ya isa Hongkong, sun bayyana kulawa da zumuncin da gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ke nuna wa Hongkong da jama'ar Hongkong.

Jaridar Wenweipo ta Hongkong ta ba da sharhi, inda aka bayyana cewa, ana ganin tunanin mai da dan Adam a matsayi mafi muhimmanci da na raya wata zaman al'umma mai jituwa da shugaba Hu ke dauka a cikin manufofin da gwamnatin tsakiya take dauka domin yankin musamman na Hongkong.

Jaridar Cheng ta Hongkong ta kuma bayyana cewa, goyon bayan da gwamnatin tsakiya ke nuna wa yankin musamman na Hongkong ya sa yawan mutanen Hongkong da suke amincewa da gwamnatin tsakiya yana ta karuwa. (Sanusi Chen)