Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-30 18:25:11    
Hong Kong a cikin shekaru 10 da suka wuce

cri

Ran 30 ga watan Yuni na shekarar 1997 da karfe 11 da minti 59 da dare, da zarar aka saukar da tutar kasar Birtaniya sannu sannu a babban zauren cibiyar taruruka da nune-nune ta Hong Kong da ke Wan Chai ta Hong Kong, sai an daga tutar kasar Sin a hankali a hankali. Daga nan ne Birtaniya ta sa aya ga mulkin mallaka na tsawon shekaru fiye da 100 a Hong Kong, Hong Kong ta shiga sabon zamani. A cikin wadannan shekaru 10 da suka wuce, Hong Kong ta sami sauye-sauye da yawa, amma abubuwa da yawa ba su canza ba.

Kafin dawowar Hong Kong a karkashin shugabancin kasar Sin, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta taba yin alkawari a tsanake cewa, za a aiwatar da manufar 'kasa daya, amma tsarin mulki 2' a Hong Kong, ba za a canza tsare-tsaren zaman al'umma da tattalin arziki da shari'a da hanyoyin zaman rayuwa da mutanen Hong Kong suke bi a da ba. An tabbatar da wadannan alkawari a cikin 'babbar doka ta yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin'.

Bayan dawowar Hong Kong a kasar Sin, a galibi dai Hong Kong ta ci gaba da aiwatar da tsarin shari'a da ta yi amfani da shi a lokacin da Birtaniya ke mulkinta, ta soke ko kuma gyara abubuwa kadan da suke da sigar musamman na mulkin mallaka. Game da wannan, shugaba Rita Fan Hsu Lai-Tai ta kwamitin kafa dokoki na Hong Kong ta yi karin bayanin cewa,'Yawancin dokokin da ake aiwatarwa kafin dawowar Hong Kong a kasar Sin sun ci gaba da aiki bayan dawowar Hong Kong a kasar Sin, sai wasu kadan ne kawai aka yi musu gyare-gyare, wadanda suka sha bamban da abubuwan da ke cikin babbar dokar Hong Kong.'

Bayan dawowar Hong Kong a kasar Sin, ci gaba da bin tsare-tsaren tattalin arziki da shari'a a Hong Kong ya sanya Hong Kong ta ci gaba da zama cibiyar duniya a fannonin kudi da jigilar kayayyaki a kan teku da kuma ciniki, haka kuma karfin takararta na ta karuwa.

Dawowar Hong Kong a kasar Sin ba ta canza hanyoyin zaman rayuwar mutanen Hong Kong sosai ba, mutanen Hong Kong suna ci gaba da kallon sukuwar dawaki da sayen tambola da shiga kasuwannin takardun hada-hadar kudi da kadarorin gidaje.

Yawancin mutanen Hong Kong suna kishin kallon sukuwar dawaki da yin fare kan dawaki, har ma ba a raba su da wadannan harkoki 2 ba. Kim K.W. Mak, darektan gudanarwa mai kula da harkokin bunkasuwa na kamfanin harkokin sukuwar dawaki na Hong Kong ya bayyana cewa,'Sukuwar dawaki ta Hong Kong ta nuna sigar musamman sosai. Bayan dawowar Hong Kong a kasar Sin, mujallar Fortune ta taba shirya dandalinta a Hong Kong. A ko wane birnin da ma'aikatan mujallar suka kai ziyara, suna fatan zaben wani wuri da ya fi nuna sigar musamman na birnin. Bayan da suka dudduba wurare da yawa a Hong Kong, sun yanke shawarar yin dandalin a filin sukuwar dawaki da ke Happy Valley. Saboda suna tsammanin cewa, wannan filin sukuwar dawaki alama ce ta Hong Kong a idanun mutanen duniya. Yin sukuwar dawaki a cibiyar birnin da aka sami manyan gine-gine a nan ya shahara a Hong Kong, ya kuma nuna sigar musamman ta Hong Kong sosai.'

A sa'i daya kuma, Hong Kong ta sami sauye-sauye, wato halin da take ciki na samun kyautatuwa sosai. A cikin wadannan shekaru 10, ta raya tattalin arzikinta yadda ya kamata, mutanen Hong Kong sun kara amincewa da asalinsu na Sinawa. Yanzu Hong Kong ta sayar da kayayyakinta zuwa babban yankin Sin ba tare da biyan haraji ba. Mutanen Hong Kong dubu daruruka sun sami aikin yi a babban yankin Sin.

Yanzu mutanen babban yankin Sin da yawa sun je Hong Kong domin yin ziyara da sayen abubuwa, sun samar da babban karfi ga Hong Kong a fannin raya aikin yawon shakatawa. Mataimakin shugaban majalisar kula da aikin yawon shakatawa ta Hong Kong Warren Tong ya bayyana cewa,'Bayan da kungiyoyin masu yawon shakatawa na babban yankin Sin suka sami damar ziyarar Hong Kong, yawan mutanen babban yankin Sin da suka kawo mana ziyara ya wuce miliyan 10 a ko wace shekara, yanzu wannan adadi ya wuce miliyan 12, wato ke nan ya wuce rabin jimlar mutanen duniya da suka kawo mana ziyara.'

A cikin shekaru 10 da suka wuce, Hong Kong da babban yankin Sin sun kara raya hulda a tsakaninsu. Ko da yake Hong Kong ta taba fuskantar rikicin kudi na Asiya da annobar ciwon SARS, amma a duk lokacin da take gamuwa da matsaloli, gwamnatin tsakiya ta kasar ta bai wa Hong Kong cikakken goyon baya, ta zama harsashi mai inganci da ke taimakawa Hong Kong domin jure wahalhalu da ci gaba da samun bunkasuwa. Yawancin mutanen Hong Kong suna ganin cewa, Hong Kong tana fuskantar kyakkyawar makoma a sakamakon goyon baya daga gwamnatin tsakiya da saurin bunkasuwar tattalin arzikin babban yankin Sin da kuma kokarin da mutanen Hong Kong suka yi.(Tasallah)