Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-30 18:07:53    
Sinawa da ke zama a kasashen waje sun shirya bukukuwan murnar cikon shekaru 10 da dawowar ikon mulkin Hongkong a kasar Sin

cri
A cikin kwanakin nan da suka wuce, ofisoshin jakadancin kasar Sin da ke kasashen waje da Sinawa wadanda suke zama a ketare sun shirya bukukuwa iri iri domin taya murnar cikon shekaru 10 da dawowar ikon mulkin Hongkong a karkashin kasar Sin.

A ran 29 ga wata, Mr. Tao Wenxue, muhimmin jami'in ofishin jakadanci na kasar Sin da ke kasar Czech ya shirya liyafa domin taya murnar cikon shekaru 10 da dawowar ikon mulkin Hongkong a kasar Sin. A gun liyafar, Mr. Tao Wenxue ya ce, a cikin shekaru 10 da suka wuce, an samu nasara wajen aiwatar da tsarin mulki iri biyu a cikin wata kasa a yankin musamman na Hongkong da manufar mutanen Hongkong ne ke mulkin Hongkong da kansu ta hanyar dimokuradiyya. Zaman rayuwar yankin musamman na Hongkong yana cikin kwanciyar hankali, tattalin arzikinsa ma yana ta samun bunkasuwa.

Bugu da kari kuma, bi da bi ne ofishin tattalin arziki da cinikayya na yankin musamman na Hongkong na kasar Sin da ke kasar Singapore da Sinawa wadanda suke zama a Canada da Amurka da Australiya sun kuma shirya bukukuwa iri iri domin taya murnar cikon shekaru 10 da dawowar ikon mulkin Hongkong a kasar Sin. (Sanusi Chen)