Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-30 17:36:40    
Hu Jintao ya duba rundunar soja ta 'yantar da jama'ar Sin da ke Hongkong

cri

A ran 30 ga wata da safe, Mr. Hu Jintao, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar, kuma shugaban kwamitin soja na kwamitin tsakiya na kasar Sin ya yi rangadin aiki a sansanin rundunar teku da ke tsibirin Stonecutters na yankin musamman na Hongkong, kuma ya duba rundunar soja ta 'yantar da jama'ar Sin da ke Hongkong.

Da misalin karfe 10 na safe ne an fara bikin duba faratin sojojin rundunar soja ta 'yantar da jama'ar Sin da ke kunshe da sojojin kasa da na teku da na sama.

Bayan bikin, Mr. Hu Jintao ya yi rangadin aiki a sansanin rundunar soja ta 'yantar da jama'ar Sin da ke Hongkong da hafsoshin rundunar, inda Mr. Hu yana fatan rundunar soja ta 'yantar da jama'ar Sin da ke Hongkong za ta ci gaba da bin babbar doka ta Hongkong da dokokin yankin musamman na Hongkong da dokar da aka kafa domin rundunar musamman.

Bugu da kari kuma, a wannan rana da safe, a otel din da yake sauka, Mr. Hu Jintao ya gana da Mr. Tung Chee Hwa, mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin kuma tsohon gwamna na farko na yankin musamman na Hongkong. (Sanusi Chen)