Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-29 18:33:07    
Beijing mai masaukin taron wasannin Olympic na janyo hankulan shahararrun masu daukar hoto na duniya

cri

Aminai 'yan Afrika, gagarumin taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008, ba ma kawai ya janyo hankulan 'yan wasa taurari na duk duniya ba, har ma ya bada sha'awa ga 'yan kasuwa masu zuba jari musammman ma ga wasu masu fasaha. Kwanakin baya bada dadewa ba, shahararrun malamai guda 10 masu daukar hoto na duniya sun zo nan birnin Beijing domin daukar kyawawan hotuna dake alamanta kyakkyawar surar birnin.

Game da birnin Beijing dai, wannan gagarumin taron wasannin Olympics na shekarar 2008, wani kasaitaccen taron wasannin motsa jiki ne; haka kuma ya kasance tamkar wani kyakkyawan dandamali ne da zai alamanta kyakkyawar fuska ta birnin Beijing. A matsayin wani sanannen birnin al'adu dake da dadadden tarihi, yanzu birnin Beijing ya rigaya ya samu bunkasuwa har ya zama wani birni dake hada da al'adu na tsohon zamani da kuma wayin kai na zamanin yau, inda ya kasance da unguwar kasuwanci ta Xi Dan, da unguwar kasuwanci ta Wangfujing da kuma unguwar kasuwanci ta Guomo da dai sauransu; Ban da wannan kuma, ya kasance da wasu wuraren al'adun gargajiya kamar na Hou Hai, da Gulou da kuma na Qianmen da dai sauransu, wadanda suke bayyana sigar musamman ta birnin Beijing. Domin bada karin haske ga aminai baki masu tarin yawa wajen fahimtar birnin Beijing da kuma kasar Sin, kwanan baya dai, kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya gudanar da wata harkar daukar hotuna dake da babban jigo a kan cewa " Birni na taron wasannin Olympics". Kwamitin ya gayyaci shahararrun malamai guda 10 masu daukar hoto na kasa da kasa ga zuwan nan Beijing domin daukar hotuna dake bayyana yanayin al'adu, wadanda kuma za a nuna su a gaban bainal jama'a.

Madam Wang Hui, mataimakiyar ministan furfaganda na kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ta fada wa wakilinmu, cewa a 'yan shekarun baya, mukan yi nune-nunen hotona na game da birnin Beijing da kuma taron wasannin Olympic na Beijing a wasu muhimman birane na ketare. Daga baya, Madam Wang Hui ta bada wani misalin cewa, a watan Oktoba na shekarar 2005, sun shirya wani nunin hotona na sabon Beijing da sabon taron wasannin Olympic a cibiyar fasaha ta Kennedy a kasar Amurka. Madam Wang ta ce, a lokacin, akwai wata mace da ta ke kallon hotunan har sau uku, tana tsayawa a gaban hotonan kuma ba ta son barin wurin nunin. Da ganin haka, sai Madam Wang ta kusance ta. Nan take, wannan mace ta duba ta cikin halih sahihanci, kuma ta tambaye ta cewa ' Ko za ku iya ba ni wannan hoto bayan nunin ? Ina so in biya kudi'. Sai Madam Wang ta fadi, cewa "Me ya sa kike sha'awar wannan hoto" ? Macen ta bada amsa, cewa " Daga wannan hoto ne na samo labari a bayansa, kuma na fahimci tarihin kasar Sin." A karshe dai, Madam Wang ta mika mata kyautar kopin wannan hoto domin shafe hawayenta. Wannan 'yar kallo mace ta jiku sosai da samun wannan kyauta.

Madam Wang Hui ta kuma furta, cewa akwai 'yan kallo da yawa da suka rubuta abubuwan da suka ji a cikin zukatansu a game da nune-nunen hotuna. Wannan dai wani dalili ne da janyo hankulan malamai masu daukar hoto ga zuwan nan Beijing domin shiga harkar da muka gudanar.

Kazalika, Madam Wang ta fadi, cewa birnin Beijing, wani birni ne dake cike da rayayyen karfi, kuma mazauna birnin suna da zafin nama kuma suna son baki. Mr. Harry Mattison yana daya daga cikin wadannan malamai masu daukar hoto ya yi farin ciki da fadin, cewa ' An haife ni a tsibirin Manhattan, wato New York, wanda girmansa bai kai na Beijing ba. A nan, na ga mazauna birnin Beijing na bin irin salon rayuwa mai ban sha'awa, wanda ya burge ni kwarai da gaske ! A 'yan kwanakin nan da suka shige, na hau keke na kai ziyara daga kananan lunguna zuwa ma'aikatar sarrafa karafuna, inda na gane wa idona manyan sauye-sauyen birnin da aka samu.'

A karshe dai, Mr. Mattison ya bayyana, cewa an samo asalin fasahar daukar hoto ne a kasar Faransa. Wani malami mai girma mai daukar hoto da ake kira Eugen Arget na kasar ya dauki hotuna masu yawan gaske wadanda suka alamanta kyakkyawan yanayin birnin Paris. A matsayin wani malami mai daukar hoto, duniyar yau na da kyaun gani kamar yadda birnin Paris yake a idona. Ina so in more dukkan kyawawan abubuwan birnin Beijing tare da mutanen duk duniya.

Yanzu, ana nan ana yin nune-nunen hotunan da wadannan malamai masu daukar hoto suka dauka, wadanda kuma suka janyo hankulan dimbin mazauna birnin da kuma masu yawon shakatawa baki. (Sani Wang )