Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-29 18:31:43    
Sinawan da ke zama a ketare suna cike da imani ga makomar Hongkong

cri

Ran 1 ga watan Yuli na shekarar da muke ciki rana ce ta cikon shekaru 10 da maido da ikon mulkin Hongkong a karkashin gwamnatin kasar Sin da kafuwar yankin musamman na Hongkong a tsanake. Kwanan baya, Sinawa wadanda suke zama a ketare sun bayyana ra'ayoyinsu na amincewa da aiwatar da "tsari iri biyu a cikin kasa daya", kuma sun nuna yabo ga cigaban da aka samu a Hongkong bayan maido da shi a kasar Sin.

Mr. Steven Wong, shugaban asusun Lin Zexu da ke kasar Amurka yana ganin cewa, ana aiwatar da "tsari iri biyu a cikin kasa daya" a Hongkong cikin nasara. Yanzu yankin musamman na Hongkon yana cikin kwanciyar hankali da bunkasuwa sakamakon aiwatar da wannan "tsari iri biyu a cikin kasa daya" a Hongkong a cikin wadannan shekaru 10 da suka wuce. Steven Wong ya ce, "Kafin shekarar 1997, mutane da yawa sun yi shakka kan alkawuran da kasar Sin ta dauka a cikin Hadaddiyar Sanarwa ta Sin da Ingila, ciki har da alkawarin 'ba za a canja tsarin Hongkong har na tsawon shekaru 50 ba' da aiwatar da 'tsari iri biyu a cikin kasa daya' da 'mutanen Hongkong ne ke mulkin Hongkong'. Amma a cikin wadannan shekaru 10 da suka wuce, na gane cewa, a hakika dai, ana aiwatar da 'tsari iri biyu a cikin kasa daya' da 'mutanen Hongkong ke mulkin Hongkong' a yankin Hongkong. 'Yan uwanmu na Hongkong suna kuma canza matsayinsu na yin shakka ko jin tsoron maido da ikon mulkin Hongkong a karkashin kasar Sin. yanzu yawan mutanen da suke amincewa da maido da ikon mulkin Hongkong a karkashin kasar Sin yana ta karuwa."

Mr. Zhao Yizhou, wani sanannen mai zane-zane na kasar Sin wanda yake yada al'adun al'ummomin kasar Sin a birnin London na kasar Ingila, kuma yake kula da sauye-sauyen da ake samu a Hongkogn yana kuma da irin wannan ra'ayi. Ya gaya wa wakilinmu cewa, "A karkashin ka'idar aiwatar da 'tsari iri biyu a cikin kasa daya', ana tabbatar da tsare-tsare masu amfani a Hongkong, alal misali, ana daidaita harkokin zaman al'ummar Hongkong bisa doka, ana sufurin jari da kwararru da kayayyakin sayarwa cikin 'yanci. Al'adu da addinai iri iri da kabilu daban-daban suke zama tare cikin lumana. Sakamakon haka, ina ganin cewa, manufar aiwatar da 'tsari iri biyu a cikin kasa daya' tana da makoma mai haske. Wannan hakikaniyar manufa ce ga yunkurin dinkuwar duk kasar Sin gaba daya cikin lumana. Tana kuma samar da sabon tunani kan yadda za a daidaita rikice-rikice da batutuwa na tarihi da suke kasancewa a sauran kasashen duniya ta hanyar zaman lafiya."

Mr. Han Junchang, shugaban kungiyar sa kaimi wajen neman dinkuwar duk kasar Sin gaba daya cikin lumana wadda ke kasar Kenya ya kuma gaya wa wakilinmu cewa, "A cikin wadannan shekaru 10 da suka wuce, yankin musamman na Hongkong ya jure jerin wahalhalu iri iri, kamar su rikicin kudi da ya auku a Asiya da annobar ciwon SARS. A gaban wadannan wahalhalu, gwamnatin tsakiya da jama'ar da ke zama a babban yanki sun taka muhimmiyar rawa wajen samar wa yankin musamman na Hongkong taimako domin kawar da wadannan wahalhalu daga Hongkong. A waje daya, tattalin arziki da kasuwanni na Hongkong suna cigaba da samun bunkasuwa kamar yadda ake fata."

Mr. Christian Siu, wani Basine ne da aka haife shi a kasar Faransa ya ce, ya san Hongkong daga bakin mahaifinsa. "An haifi mahaifina a Hongkong. Kafin shekarar 1997, ya taba komawa Hongkong har sau da dama. Ya gaya mini cewa, a yankin Hongkong, ana aiwatar da tsarin jari-hujja sosai kamar yadda ake gani a kasar Ingila. Bayan shekarar 1997, ya kuma sake komawa Hongkong sau daya. Ya ce, ba a sauya tsarin jari-hujja a Hongkong ba. Ya kuma yaba wa Hongkong cewa Hongkong yana da kyau, ya shawarce ni da in kai wa Hongkong ziyara."

Mr. C.H.Hua, shugaban kungiyar sa kaimi wajen neman dinkuwar duk kasar Sin cikin lumana da ke birnin New York na kasar Amurka yana kuma cike da imani ga makomar Hongkong. Ya gaya wa wakilinmu cewa, "Idan ana kan matsayi daidai, dukkan mutane, ciki har da madam Thatcher, tsohuwar firayin ministar kasar Ingila suna ganin cewa, maido da ikon mulkin Hongkong a karkashin kasar Sin da aiwatar da 'tsari iri biyu a kasa daya' a Hongkong ya samu nasara sosai. Ina cike da imani ga makomar Hongkong, ina kuma cike da imani ga al'ummar Sinawa gaba daya." (Sanusi Chen)