Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-29 18:31:37    
Ana samar da dazuzzuka cikin sauri a birane da garuruwa na kasar Sin

cri

A galibi dai, ya kamata, a ga dazuzzuka a kan tuddai ko duwatsu wadanda ke da nisa daga garuruwa da birane, kuma ba safai a kan gan su a cikin garuruwa da birane ba. Amma a cikin shekarun nan da suka gabata, an samar da dazuzzuka cikin sauri a garuruwa da birane na kasar Sin da yawa don kyautata muhallin zaman rayuwar jama'a. Kwararru sun nuna cewa, yin haka zai ba da taimako ga samun ci gaba mai dorewa don raya garuruwa da birane na kasar, kuma zai samar musu da dukiya mai yawa don kiyaye yanakin kasa.

A kwanakin baya, an kira taron dandalin tattaunawa kan dazuzukan garuruwa da birane na kasar Sain a karo na 4 a birnin Chengdu, fadar gwamnatin lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin. Inda aka bayar da lambar girmamawa ta "biranen Sin masu dazuzzuka" ga birane hudu wadanda suka hada da birnin Chengdu. A gun taron, Malam Mahendra Joshi, jami'i mai kula da manyan ayyuka na sakatariyar taron dandalin tattaunawa kan dazuzzuka na majalisar dinkin duniya ya nuna babban yabo ga aiki da kasar Sin ke yi wajen samar da dazuzzuka. Ya ce, "irin kokari da gwamnatin kasar Sin da kananan hukumominta ke yi wajen dasa bishiyoyi a garuruwa da birane da kuma duk kasar ya shere ni sosai, kuma ya shiga zuciyata kwarai."

An ruwaito cewa, kullum birnin Chengdu yana kokari sosai wajen kyautata da kiyaye tsarin yanayin dazuzzuka. A cikin shekaru 20 da suka wuce, shingen bishiyoyi ya karu daga kashi 23 cikin dari zuwa kashi 36 cikin dari a birnin. An kiyasta cewa, an samu 'ya'yan itatuwa masu dimbin yawa daga dazuzzuka don samar da su ga mazaunan birnin, yawan hatsi da kayayyakin lambu da aka samu daga karkarar birnin ma ya karu da kashi 15 cikin dari, haka kuma yawan makamashi da aka yi amfani da shi ya ragu da kashi 10 zuwa 15 cikin dari.

Magajin gari ko wakilai na garuruwa da birane na kasar Sin 124 sun halarci taron dandalin tattaunawar, kuma sun mai da hankali sosai ga aikin samar da dazuzzuka a garuruwa da birane. Malam Duocizhu, magajin gari na Lhasa, fadar gwamnatin jihar Tibet mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kasar Sin ya bayyana cewa, makasudinsa na halartar wannan taro shi ne domin yin koyi da sakamako da birnin Chengdu ya samu, ta yadda za a gaggauta dasa bishiyoyi a birnin Lhasa da kyautata muhallin zaman rayuwar jama'a. Ya ce, "bisa matsayin birnin Lhasa na kiyaye yanayin kasa a Sin, ana kokari sosai wajen raya birnin da ya zama birnin yawon shakatawa mai sigar musamman a kan duwatsu. Ta hanyar koyi da sakamako da birnin Chengdu ya samu, mun aza harsashi mai kyau ga samar da dazuzzuka a birninmu, don kiyaye da kyautata yanayin kasa a fannin sararin sama da ruwa da sauransu. "

Malam Ge Honglin, magajin gari na birnin Chengdu yana ganin cewa, ta hanyar samar da dazuzzuka a birni, an gaggauta bunkasa harkokin tattalin arzikin birninsa. Amma kamata ya yi, a samar da dazuzuka a garuruwa da birane bisa halin da ake ciki. Madam Michelle Gauthier, jami'a mai kula da dazuzzuka na ofishin kiyaye dazuzzuka na hukumar abinci da aikin noma ta majalisar dinkin duniya wato FAO ta ce, hanyar da kasar Sin ke bi wajen samar da dazuzzuka a garuruwa da biranenta tana da kyau, amma ya kamata, a kafa tsarin samar da dazuzzuka bisa halayen musamman daban daban da ake ciki a garuruwa da birane. Ta kara da cewa, "sabo da halaye da ake ciki a garuruwa da birane sun sha banban, shi ya sa ko wanensu ya iya samo hanyar da yake bi don samar da dazuzzuka yadda ya kamata. Ta haka kuma za a iya kiyaye halayensu na sigar musamman."

A lokacin karshen taron dandalin tattaunawar, wakilai mahalartan taron sun bayar da wata sanarwa, wadda a ciki aka gabatar da cewa, ya kamata, a nuna himma ga samar da dazuzuka a garuruwa da birane bisa halayen musamman da suke ciki. Mun hakkake cewa, za a ci gaba da nuna himma wajen samar da dazuzzuka a garuruwa da birane na kasar Sin. (Halilu)