Yau shugaban kasar Sin, Hu Jintao ya isa Hongkong, don halartar bikin murnar cikon shekaru 10 da Sin ta maido da mulkinta a Hongkong da kuma bikin rantsar da sabuwar gwamnatin yankin musamman ta Hongkong.
Gwamnan yankin musamman na Hongkong, Donald Tsang da sauran muhimman jami'an Hongkong tare da jami'an hukumomin gwamnatin tsakiya na kasar Sin da ke Hongkong sun je filin jirgin sama don taryar Hu Jintao da 'yan rakiyarsa.
Ranar 1 ga watan Yuli mai zuwa rana ce ta cikon shekaru 10 da Sin ta maido da mulkinta a Hongkong. A shekaru 10 da suka wuce, gwamnatin kasar Sin ta maido da mulkinta a Hongkong, kuma yankin musamman na Hongkong ya kafu a hukunce.(Lubabatu)
|