Bisa kididdigar da ma'aikatar harkokin hanyar dogo ta kasar Sin ta yi, an ce, yawan fasinjojin da aka yi sufurinsu ta hanyar dogo ta Qinghai-Tibet ya kai fiye da miliyan 1.3
Hanyar dogo ta Qinghai-Tibet hanyar dogo ce da ta fi tsawo, kuma ta fi tsayi daga leburin teku daga cikin hanyoyin dogo da suke tuddai a duk fadin kasashen duniya. A cikin shekara daya da ta wuce bayan kaddamar da wannan hanyar dogo, injuna da ma'aikata da fasahohin yin amfani da ita sun ci jarrabawa iri iri da sauye-sauyen yanayi suka yi musu. Har yanzu ba a gamu da hadarurukan zirga-zirgar jiragen kasa, kuma ma'aikata da fasinjoji suna cikin koshin lafiya. Bugu da kari kuma, saurin jiragen kasa da ke tafiya a kan wannan hanyar dogo ta Qinghai-Tibet ya kai kilomita dari 1 a kowace awa. (Sanusi Chen)
|