Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-28 19:08:27    
Ana aiwatar da manufar "tsari iri biyu a kasa daya" a Hongkong kamar yadda ake fata

cri

Ran 1 ga watan Yuli mai zuwa rana ce ta cikon shekaru 10 da maido da ikon mulkin Hongkong a karkashin gwamnatin kasar Sin da kafuwar yankin musamman na Hongkong na kasar Sin a tsanake. A matsayin cibiyar duniya ta kudi da cinikayya da jigilar kayayyaki da ta yawon shakatawa, sauye-sauyen da aka samu a yankin musamman na Hongkong bayan maido da ikon mulkinsa a karkashin kasar Sin suna jawo hankulan mutanen duniya sosai. Yanzu ga wani bayanin da wakilanmu suka aiko mana daga wurare daban-daban na duniya.

Shehun malami Li Cheng wanda yake nazarin batutuwan kasar Sin a cibiyar Brookings ta kasar Amurka yana ganin cewa, a cikin shekaru 10 da suka wuce, manufar "aiwatar da tsari iri biyu a cikin kasa daya" da ake aiwatar da ita a Hongkong ta samu nasara sosai. Mr. Li Cheng ya ce, "A ganina, a hakika dai, manufar aiwatar da 'tsari iri biyu a cikin kasa daya' ta samu nasara sosai a Hongkong. Ba ma kawai 'yan kallo da suke zama a kasashen waje kamar ni suke gane wannan ba, har ma jama'ar Hongkong suke gaya maka kwatankwacin abubuwan da ka gani a Hongkong idan kai su ziyara."

Shehun malami Li Cheng ya ce, a fannin harkokin siyasa, yana kasancewa da 'yanci da tsarin bayar wa jama'a labaru a fili a Hongkong kamar yadda aka saba yi a da. A waje daya kuma, tsarin dimokuradiyya na Hongkong yana ta samun cigaba. Bugu da kari kuma, shehun malami Li Cheng ya jaddada cewa, tattalin arzikin Hongkong ya samu cigaba sosai a cikin shekaru 10 da suka wuce. "Ko shakka babu, yankin musamman na Hongkong ya sha wahalhalu da yawa a cikin shekaru 10 da suka wuce, kamar annobar ciwon SARS da ya auku a shekarar 2003, rikicin kudi da ya auku a yankin kudu maso gabashin Asiya a shekarar 1997. Amma a hakika dai, tattalin arzikin Hongkong yana ta samun cigaba."

Babban alkali Shi Jiuyong, wani dan kasar Sin wanda yanzu ke aiki a kotun duniya da ke birnin Hague na kasar Holland ya taba halartar shawarwarin da aka yi a tsakanin kasashen Sin da Ingila kan batun Hongkong da aikin tsara shirin Babbar Doka ta Hongkong. Mr. Shi ya ce, hakikanan abubuwa sun shaida cewa, a cikin shekaru 10 da suka wuce bayan da aka maido da ikon mulkin Hongkong a karkashin gwamnatin kasar Sin, yankin musamman na Hongkong ya ci jarrabawa iri iri, har yanzu yana kan matsayin cibiyar duniya ta kudi da cinikayya da sufurin kayayyaki. Wannan nasara ne da gwamnatin kasar Sin ta samu domin aiwatar da 'tsari iri biyu a cikin kasa daya'. Mr. Shi ya ce, "An tsara Babbar Doka ta Hongkong ne bisa Hadaddiyar Sanarwa ta Sin da Ingila. Abubuwan da ke cikin Babbar Doka ta Hongkong suna bayyana abubuwan da ke cikin wannan Hadaddiyar Sanarwa ta Sin da Ingila gaba daya. Sabo da haka, babu cacar baki da ake yi. Wannan kuma ya shaida cewa, manufar aiwatar da 'tsari iri biyu a cikin kasa daya' tana daidai. 'Babbar Doka ta Hongkong' da 'Hadaddiyar Sanarwa ta Sin da Ingila' ma suna da rayuwa."

Sauye-sauyen da aka samu a Hongkong bayan maido da ikon mulkin kansa a karkashin gwamnatin kasar Sin ya samu yabo sosai daga kasashen duniya. Mr. Shi Jiuyong ya gaya wa wakilinmu cewa, yawancin jami'ai da mutane na Hongkong da ya taba tuntubarsu suna farin ciki ga halin da ake ciki a Hongkong. Ya ce, "A lokacin farko dai, mutanen Hongkong suna da damuwa, wasu daga cikinsu sun kaura zuwa kasashen waje, kamar Australiya da Amurka da Canada. Amma yanzu mutane da yawa daga cikinsu suna ta komawa Hongkong a cikin wadannan shekaru 10 da suka wuce domin sun gane cewa, Hongkong yana da kyau. Alal misali, wasu iyalaina wadanda suke zama a Hongkong sun taba kaurawa zuwa Australiya da Canada, amma yanzu dukkansu sun koma Hongkong."

Mr. Jack Maisano, shugaban kungiyar kasuwanci ta Amurka da ke Hongkong ya gaya wa wakilinmu cewa, "Membobin kungiyarmu suna cike da imani ga makomar Hongkong. A tsakanin yankin musamman na Hongkong da babban yanki na kasar Sin, a cikin 'yanci ne ana sufurin kayayyaki da kudade da kwararru da yin sana'o'in ba da hidimomi da na ba da shawara. Ina ganin cewa, Hongkong yana da wata makoma mai haske a fannin tattalin arziki." (Sanusi Chen)