A bikin bude taron shekara shekara na kwamitin kungiyar bankin raya Afrika na shekara ta 2007 da aka yi a watan Mayu na wannan shekara,Firayim Minista na kasar Sin ya bayyana cewa Gwamnatin Kasar Sin ta bayyana manufofi takwas da ta tsara kan kasashen Afrika ciki har da kasar Sin za ta ba da karin taimako ga kasashen Afrika da yafe basussuka na kasashen dake fama da basusuka masu tsananni da kuma kasashen marasa cigaba wajen masana'antu na Afrika,da bude kasuwanninta ga Afrika,da karfafa hadin kan kasar Sin da Afrika wajen tattalin arziki da zamantakewa da sauran fannoni da nuna goyon baya ga kasashen Afrika wajen raya kasa.Ya ce kasar Sin za ta cika alkawarin da ta dauka a dukkan fannoni,kuma za ta yi kokare tare da kasashen Afrika wajen tabbatar da wadannan manufofi.Ga cikakken jawabin da Firayim Minista Wen Jiabao ya yi.
Yau a nan birnin Shanghai na kasar Sin an yi taron shekara shekara na kwamitin kungiyar bankin raya Afrika na shekara ta 2007 inda za a tattauna muhimman manufofin bunkasa tattalin arziki da zamantakewa na Afrika.A makwafin gwamnatin kasar Sin da jama'arta ina taya murnar kiran taron nan cikin gaggarumin hali,ina maraba da zuwa kasashe mambobi na kwamitin da tawagogi domin halartar taron nan,kuma Ina nuna godiya ga shugaba Kagame da shugaba Pires da Shugaba Lawalumanana da su shiga wannan bikin bude taron shekara shekara.A kan matsayin wata hukumar kudade ta duniya ta wani bangare,a cikin shekaru sama da 40 da suka gabata,bankin raya Afrika ya yi kokari ba tare da gajiya ba har ma ya samu gaggarumar nasara wajen daukaka cigaban tattalin arziki da zamantakewa na Afrika.Kasashe manbobin kwamitin sun nuna kwazo da himma wajen tattara kudade domin bunkasa kasashen Afrika harma sun ba da shawarwari da manufofi,hadin kan kasa da kasa na kara karfi a kwana a tashi.A cikin shekaru biyu na baya,A karkashin jagorancin shugaban bankin raya Afrika Kaberuka kuma bisa taimako daga kasashe manbobin kwamitin,Bankin raya Afrika ya kawo sauyi,ya kokarta wajen samo sabbin hanyoyin ba da hiddima ga kasashen Afrika.Kiran taron nan babu shakka zai cigaba da inganta bankin Afrika da kara rawar da bankin raya Afrika zai taka da kuma tasirinsa.
Yayin da duniya ta ke samu kungiyoyi masu karfi da dama da manufofin tattalin arziki na kara hadewa,Afrika ta samu zarafin bunkasuwa haka kuma tana fuskantar kalubale.Mun yi farin ciki da ganin haka,cikin shekarun baya baya,halin zaman lafiya da kwanciyar hankali na cigaba da inganta,hadin kan bangarori da hade haden manufofin tattalin arziki na ci gaba lami lafiya,tattalin arziki na kara bunkasa,zamantakewa na rika samun cigaba,Afrika ta samu babban cigaba wajen raya kasashensu.A sa'I daya kamata ya yi a mai da hankali kan wasu matsaloli,nauyin da ke bisa wuyan Afrika wajen bunkasa tattalin arziki da zamantakewa har wa yau dai ya yi yawa,haka kuma Afrika tana da wahaloli da dama wajen cimma makasudinta na raya kasa na shekaru dubu masu zuwa.Karin cigaban Afrika na bukatar kokarin da ita kanta za ta yi,haka kuma kuma yana bukatar goyon baya da taimako daga sauran kasashen duniya.Mun yi kira ga kasashen duniya musamman kasashe masu cigaban masana'antu da su cika alkawuran da suka dauka kan kasashen Afrika cikin tsanaki da kuma dauki takamaman matakai wajen yafe basussuka da sharudan cinikayya da ba da iznin shiga kasuwanni da taimakon fasaha ta yadda za su taimaka wa kasashen Afrika wajen kara karfinsu na raya kasa cikin yanci da samun dauwamamen cigaba wajen tattalin arziki da zamantakewa.
Da akwai zumuncin al'ada mai danko tsakanin Sin da Afrika,da sahihiyar zuciya gwamnatin Sin da jama'arta suna goyon bayan kasashen Afrika wajen samu zaman lafiya da bunkasuwa.A cikin shekaru fiye da hamsin bayan sabuwar kasar Sin ta kulla huldar jakadanci da kasashen Afrika,Kasar Sin ta taimaka wajen sanya manyan ayyuka da ayyukan jin dadin jama'a sama da 900 a kasashen Afrika, gwamnatin kasar Sin ta ba kyautar kudi ga dalibai fiye da dubu ashirin na kasashe 50 na Afrika,ta aike da masu aikin jiyya zuwa kasashe 47 na Afrika da yawan zuwa masu aikin jiyya ya kai dubu 16,marasa lafiya da suka warkar da su sun kai miliyan 180.Kasar Sin ta soke harajin kwasta kan kayayyakin da wasu kasashen Afrika marasa cigaban masana'antu ke fitarwa zuwa kasar Sin,ta haka kayayyakin Afrika sun shiga kasuwannin kasar Sin cikin sauki.gwamnatin Sin ta kuma dauki matakai masu amfani wajen sassauta basussuka da kasashen Afrika suka ci,bashin da kasar Sin ta yafe ga kasashen Afrika ya kai kudin Sin Renminbi Yuan biliyan 10.9.A halin yanzu gwamnatin kasar Sin tana nan tana shirin yafe wasu basussuka daban da darajarsu ta kai kudin Sin Renminbi Yuan biliyan goma.A hakika hadin kai na taimakon juna tsakanin Kasar Sin da kasashen Afrika a fannoni da dama ya kawo fa'ida mai amfani ga jama'a na bangarori biyu.
A cikin shekarun baya,hadin kan aminci dake tsakanin Sin da Afrika na rika samun bunkasuwa.A watan Nuwanba na shekara ta 2006,an samu nasarar kira taron koli na Beijing na tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da Afrika.Shugabanni na Sin da na kasashen Afrika sun amince da kafa sabuwar dangantaka ta kawaye tsakaninsu bisa tushen daidaici da amincewar juna a fannin siyasa da taimakon juna da samu nasara tare a fannin tattalin arziki da yin mu'amala da koyi da juna a fannin al'adu,haka kuma sun tsara shirye-shiryen hadin kai na tsakanin Sin da Afrika a cikin shekaru uku masu zuwa.Gwamnatin Kasar Sin ta bayyana muhimman manufofi guda takwas da ta tsara kan kasashen Afrika wato za ta ba da karin taimako ga Afrika da yafe basussuka na kasashe masu bin basusuka mafi yawa da kasashe marasa cigaban masana'antu da bude kasuwanninta ga Afrika,da karfafa hadin kan kasar Sin da kasashen Afrika a fannin tattalin arziki da zamantakewa da sauran fannoni,da nuna goyon bayan kasashen Afrika wajen raya kasa.Za mu cika alkawuran da muka dauka daga dukkan fannoni,tare da kasashen Afrika za mu yi kokarin tabbatar da wadannan manufofin.
Wajen karfafa hadin kai a tsakanin Sin da Afrika,kamata ya yi a sabunta hanyoyin da ake bi na hadin kai da kara karfin hadin kai ta yadda za su taimaka juna da samu nasara tare..Dole ne a hada taimakon gwamnati da hadin kan masana'antu tare
|