Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-28 15:22:24    
An shirya nune-nunen tallace-tallacen sinim a Hongkong

cri
Daga ranar 27 ga wannan wata, a gidan tanadin takardu da kayayyaki dangane da sinima na Hongkong, an yi nunin takardun tallace-tallacen sinima masu daraja sosai da yawa da aka bayar tun daga shekarar 1948 har zuwa yanzu, ana fatan cewa, ta hanyar nunin nan, za a iya taimaka wa samarin da za su fahimci tarihin raya sinima a Hongkong.

A gun nunin, an zabi takardun tallace-tallacen sinima da aka tanada a gidan tanadin takardu da kayayyaki masu daraja sosai dangane da sinima da yawansu ya kai 200, daga cikinsu da akwai wata takardar tallace-tallacen sinima mai suna "kofar Jingwu" da wani mashahurin dan wasan sinima Mr Li Xiaolong da ya zama babban dan wasa a cikinta tare da takardar tallace-tallacen sinimar da mai jagorancin wasan sinima Mr Xu Ke ya ba da jagora, wato sinima mai suna Huang Feihong.

Tun daga ranar bude kofar gidan tanadin takardu da kayayyaki dangane da sinima har zuwa yanzu, an riga an tattara takardun tallace-tallacen sinima da yawansu ya kai dubu 4 ko fiye, wadanda suka ba da shaida ga tarihin raya sinima a Hongkong cikin shekaru 10, kuma sun bayyana sifofin Hongkong da ke zamani daban daban.(Halima)