Ran 1 ga watan Yuli na bana rana ce da ta cika shekaru 10 da kafa yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin. Haka kuma ranar nan rana ce da ta cika shekaru 10 da kafa hukumar kwamishinan musamman ta ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin a Hong Kong. A gabannin ranar nan, wakilin gidan rediyo kasar Sin ya kai ziyara ga Malam Lu Xinhua, kwamishinan musamman na hukumar don jin ta bakinsa dangane da aiki da sakamako da hukumarsa ta samu a cikin shekarun nan 10 da suka wuce.
A karkashin "tsarin dokoki na Jamhuriyar Jama'ar Sin kan yankin musamman na Hong Kong, babban aiki da hukumar kwamishinan musamman ta ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ke yi a Hong Kong shi ne taimaka wa gwamnatin Hong Kong wajen daidaita batutuwan diplomasiya. Malam Lu ya nuna babban yabo ga kyakkyawan sakamako da hukumarsa ta samu a fannin diplomasiya a cikin shekaru nan 10 da suka wuce. Ya ce, "da mu waiwayo shekarun nan 10 da suka wuce, hukumarmu ta aiwatar da ka'idoji game da "kasa daya tsarin mulki iri biyu, da kula da harkoki da mutanen Hong Kong ke yi su da kansu, da gudanar da ikon kai sosai a fannin diplomasiya, kuma ta sami kyakkyawan sakamako mai tsoka a cikin shekarun nan 10."
Bayan haka malam Lu Xinhua ya kara da cewa, hukumar ta sami babban ci gaba wajen taimaka wa hukumar Hong Kong don shiga cikin kungiyoyin kasa da kasa da halartar tarurrukan kasa da kasa. Ya bayyana cewa, "a shekarun nan 10 da suka wuce, hukumarmu ta taimaki gwamnatin Hong Kong wajen halartar tarurrukan kasa da kasa sama da 800, da shirya tarurrukan kasa da kasa da yawansu ya wuce 60 a Hong Kong, sa'an nan ta bai wa gwamnatin Hong Kong taimako wajen shiga kungiyoyin kasa da kasa sama da 50. Ban da wadannan kuma daga cikin manyan tarurrukan kasa da kasa da aka shirya a Hong Kong, akwai taron ministoci na karo na 6 na kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO da ya zama wani taro ne mai cin nasara sosai."
Haka kuma Malam Lu Xinhua ya nuna babban yabo ga hadin kai da ake yi a tsakanin hukumarsa da gwamnatin Hong Kong. Ya ci gaba da cewa, yanzu, yawan kasashe da suka riga suka cim ma yarjejeniyoyi da abin ya shafa a tsakaninsu da Hong Kong ya kai 134. Ya ce, Hong Kong cibiyar aikin kudi ne, yana ma'amala da wurare daban daban na duniya, sabo da haka makasudin aikin hukumarmu shi ne domin tabbatar da Hong Kong da ya tsaya kan matsayinsa na cibiyar kudi da cinikayya da jigilar kayayyaki da yawon shakatawa a duniya bisa taimakon kasar Sin, sa'an nan a kara daga matsayin Hong Kong a duniya. Malam Lu Xinhua ya bayyana cewa, "Hong Kong cibiyar aikin kudi ne, yana ma'amala da wuraren duniya daban daban a fannin aikin kudi. Ya kafa ofisoshinsa mai kula da harkokin tattalin arziki da cinikayya sama da 10 a duniya, wadanda ke ma'amala da ofisoshin jakadanci na kasar Sin sosai. Muna so mu ci gaba da daga matsayin Hong Kong a duniya. Kyakkyawan sakamako da Hong Kong ya samu a fannin diplomasiya ya jawo hankulan mutane. Madam Margaret Chun ta ci zaben zaman babban direktan hukumar kiwon lafiya ta duniya, wannan sakamako ne da aka samu bisa babban goyon baya da kasar Sin ta nuna."
Ranar cika shekaru 10 da aka komo da Hong Kong a karkashin mulkin kasar Sin na kusantowa, Malam Lu Xinhua ya yi imani cewa, bisa kokari da hukumar kwamishinan musamman ta ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin da gwamantin Hong Kong da sauran bangarori ke yi, jama'ar Hong Kong za su ci gaba da nuna amincewa ga kasar Sin mahaifiyarsu. (Halilu)
|