Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-27 17:35:28    
Manufar "aiwatar da tsari iri 2 a cikin kasa daya" zai sa kaimi wajen dinkuwar duk kasar Sin gaba daya

cri

A ran 27 ga wata, Mr. Yang Yi, kakakin ofishin kula da harkokin Taiwan na majalisar gudunarwa ta kasar Sin ya bayyana cewa, yayin da ake aiwatar da manufar "aiwatar da tsari iri 2 a cikin kasa daya" a yankin musamman na Hongkong cikin nasara, yawan 'yan uwanmu na Taiwan da suke fahimta da kuma amincewa da wannan manufa tana ta karuwa, sabo da haka, irin wannan nasara za ta sa kaimi wajen dinkuwar duk kasar Sin gaba daya cikin lumana.

A gun wani taron manema labaru da aka saba yi a nan birnin Beijing, Mr. Yang ya ce, a cikin shekaru 10 da suka wuce bayan maido da yankin Hongkong a karkashin mulkin kasar Sin, ana tsayawa kan manufofin "aiwatar da tsari iri biyu a cikin kasa daya" da "'yan Hongkong ne ke mulkin Hongkong su da kansu" a yankin musamman na Hongkong, halin kwanciyar hankali da na bunkasuwa da ake ciki a yankin Hongkong ya samu ingantuwa da cigaba. Yankin musamman na Hongkong ma ya samu sakamako da yawa da suke jawo hankulan duk duniya. A waje daya, yankin musamman na Hongkon yana taka muhimmiyar rawar da ita kadai za ta iya takawa a tsakanin babban yanki da lardin Taiwan na kasar Sin. Yawan mutanen Taiwan da suke zuwa babban yanki ta yankin Hongkong ya kai kimanin miliyan 3 a kowace shekara. Jimlar cinikin da ake yi a tsakanin babban yanki da Taiwan ta yankin Hongkong ma ta kai dolar Amurka fiye da biliyan 10 a kowace shekara. (Sanusi Chen)