Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-27 17:42:09    
Wani mashahurin mawallafi na zamanin yau na kasar Sin mai suna He Jingzhi

cri

Mr He Jingzhi shi ne mashahurin mawallafin da ke da suna sosai a kasar Sin , kuma yana daya daga cikin masu wallafa rubutattun wakoki wadanda suka ba da tasiri sosai a kasar Sin. Littattafai da wakokin da ya wallafa a shekaru 40 zuwa 50 na karnin da ya wuce, har wa yau dai suna jawo sha'awar mutane sosai, kuma ya himmantar da samari masu aikin wallafe-wallafe daga zuri'a zuwa zuri'a na kasar Sin.

jama'a, abin da kuke saurara yanzu shi ne wani kashi na shahararren wasan kwaikwayo da aka nuna tare da wake-wake da kide-kide mai suna Bai Maonu, wato wata yarinya mai farin gashin kai. Mr He Jingzhi yana daya daga cikin mawallafan wasan, a kasar Sin, ba a yi rashin nuna wasan cikin dogon lokaci ba. Wasan tana bayyana wani labari cewa, a shekaru 30 zuwa 40 na karnin da ya shige, wata yarinya mai suna Xi'er ta sha fama da wulakancin matalautan kasa, kuma mahaifinsa mai suna Yang Bailao ya kashe kansa bisa sakamakon fama da azaba mai tsanani sosai, ba abin da za ta yi, sai yarinyar Xi'er ta ga tilashin tilashi ne ta yi gudun hijira zuwa manyan tsaunuka, kodayake ita ce yarinya, amma gashin kanta ya yi fari sosai. Amma bayan wasu shekarun da suka wuce, rundunar soja da ke karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta tumbuke mulkin matalautan kasa, yarinyar Xi'er ta sami 'yanci, ta yi sabon zaman rayuwa, kuma ta koma gida daga manyan tsaunuka.

Lokacin da Mr He Jingzhi da ke da shekaru 83 da haihuwa ya waiwayi lokacin da ya soma wallafa labarin, ya burge sosai ya bayyana cewa, wasan Bai Maonu ya bayyana mana wani labari mai ban mamaki. Na rubuta labarin ne bisa abubuwan gaskiya da suka faru a tsohuwar kasar Sin, wato bayan da rundunar soja ta neman kwatar 'yancin jama'ar kasar Sin da jam"iyyar kwaminis ta kasar Sin suka sauka wani kauyen da Bai Maonu take zama, sai an 'yantar da manoman da suke fama da wulakancin matalautan kasa. Lokacin da nake rubuta labarin, na mai da hankali sosai da sosai, kuma na waiwayi wulakancin da manoma suke fama da shi da kuma farin ciki da manoman suke yi bisa sakamakon samun 'yancin kai a birnin Yan'an, sai na yi kuka sosai har da zubar da hawaye.

An haifi Mr He Jingzhi a wani kauyen da ke manyan tsaunuka a gabashin kasar Sin a shekarar 1924, a shekaru 30 zuwa 40 na karnin da ya shige, kasar Japan ta kai hari a kasar Sin, garinsa ya zama fagen yaki mai muhimmanci wajen yin dagiya da harin Japan, tamkar yadda sauran mutanen kasar sin suke yi, saurayi He Jingzhi ya bari gidansa ya yi yawon gudun hijira a lardin Hubei da sauran wurare tare da fushin da ya yi wa makiyan Japan. A wannan lokaci, ya soma wallafa wakoki ta hanyar yin amfani da abubuwan da ya ji ya gani . A shekarar 1940, Mr He Jingzhi ya sauka birnin Yan'an wanda ke karkashin mulkin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, sa'annan kuma ya soma karatu a kolejin koyar da ilmin fasahohi da adabi na Lu Xun, daga nan sai ya kama aikin wallafe-wallafe.

Ya taba wallafa littattafai da wakoki da yawa, musamman ma wakoki guda biyu da ya wallafa su fi samun suna sosai, wata wakar da ke cikinsu tana da suna cewa, "Dawowarmu a Yan'an", wata daban tana da suna cewa, "Rera wakoki da babbar murya". Wakokin biyu suna bisa matsayi mai muhimmanci na dandalin wakoki na kasar Sin, Shi ya sa Mr He Jingzhi ya yi suna sosai a kasar Sin.

Ya bayyana cewa, ya kamata ka wallafa littattafai da wakoki bisa abubuwan da ka ji ka gani sosai. Ya ce,wakoki biyun da na wallafa sun bayyana abubuwan gaskiya da na ji na gani , sun kuma bayyana abubuwan da na waiwayo a lokacin da na shiga juyin juya hali, na bayyana abubuwan don nuna sahihiyar zuciyata ga kasar mahaifa.

Matarsa ita ce wata shaharariyyar mawallafiya, dukkansu sun sami sakamako da yawa, har wa yau dai suna ci gaba da wallafe-wallafe, kuma suna ba da taimako ga samarin da suke son aikin wallafe-wallafe.(Halima)