Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-27 17:30:27    
Kamfanin dillancin labaru na Xinhua

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun Sanusi Isah Dankaba, wanda ya fito daga birnin Keffi da ke jihar Nasarawa, tarayyar Nijeriya, wanda kuma ke sauraronmu a kullum. Sanusi ya sha ba mu tambayoyinsa, kuma a kwanan baya, a cikin wata wasikar da ya turo mana, ya ce, Xinhua shi ne kamfanin dillancin labarun gwamnatin kasar Sin wanda aka dorawa nauyin samo labaru ciki da wajen kasar Sin, shin yaushe ne aka kafa wannan kamfani kuma a yanzu kasashe nawa yake da ofisoshi, sa'an nan mutane nawa suke aiki karkashin wannan kamfani? Masu sauraro, idan kuna sauraron labaranmu a kullum, to, ku kan ji mun ce, "wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya ruwaito mana labari cewa?", haka ne, Xinhua babban kamfanin dillancin labaru ne na jamhuriyar jama'ar Sin. Domin amsa tambayar Sanusi Isah dankaba, a cikin shirinmu na yau, bari mu dan gutsura muku tarihin wannan babban kamfanin dillancin labaru na kasar Sin.

Kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya samo asalinsa ne daga "kamfanin dillancin labaru na jar kasar Sin" wanda ya kafu a watan Nuwamba na shekarar 1931. Sa'an nan, a shekarar 1937, an canja sunansa zuwa "Xinhua" da ake amfani da shi a yanzu. Bayan kafuwar jamhuriyar jama'ar Sin, musamman ma bayan da Sin ta fara aiwatar manufar bude kofa ga duniya da yin gyare-gyare a gida a shekarar 1978, harkokin da Xinhua ke gudanarwa sai dinga bunkasa suke yi.

Yanzu kamfanin dillancin labaru na Xinhua yana da ma'aikatan da yawansu ya kai fiye da dubu 13. Hedkwatar Xinhua yana birnin Beijing, babban birnin kasar Sin. Ban da wannan, yana kuma da rassansa 33 a duk fadin kasar Sin, ciki har da Hongkong da Macao, tare kuma da ofisoshin wakilansa a birane manya da matsakaita sama da 50. A kasashen ketare kuma, Xinhua ya kafa rassa a kasashe da shiyyoyi fiye da 100, ciki har da birnin Lagos da ke tarayyar Nijeriya.

Xinhua yana da hanyoyi da dama na bayar da labaransa. A nan gida, yana samar da labarai ga birane da garuruwa da jaridu da kuma gidajen rediyo da kuma gidajen telebijin. Bayan haka, yana kuma bayar da labaransa iri iri da suka hada da bayanai da hotuna da audio da vedio da dai sauransu cikin awa 24 ko wace rana ba tare da tsayawa ba ga kasashen duniya daban daban cikin harsuna takwas, ciki har da Sinanci da Turanci da Faransanci da Rashanci da Spainyanci da Larabci da yaren Portugal da kuma Japonanci. A kowace rana, yawan labaran da Xinhua ke bayarwa ya kai fiye da dubu 11, tare kuma da hotuna sama da 900 da kuma labaran irin na Audio da Video fiye da 20. Masu amfani da internet na iya shiga shafin internet na Xinhua don karanta labaran da Xinhua ya samo daga gida da kuma kasashen duniya, wato www.xinhuanet.com.

Xinhua yana kuma buga jaridu iri iri da yawansu ya wuce 20, kuma ko wace shekara, ya kan kuma buga littattafai sama da 400 da ke shafar labarai da siyasa.

Xinhua shi kuma mamba ne na kungiyoyin labaran duniya da dama, ya kuma daddale yarjejeniyoyi tare da takwarorinsa na kasashe da shiyyoyin duniya sama da 100 dangane da musanyar labarai da ma'amalar ma'aikata da hadin gwiwar fasaha.(Lubabatu)