Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-27 16:13:03    
Yawan kudin jari da Hong Kong ya zuba a Shenzhen na Sin ya wuce dalar Amurka biliyan 42

cri
Bisa kididdigar hukumar kula da harkokin masana'antu da kasuwanci ta birnin Shenzhen da ke a kudancin kasar Sin ta yi, an ce, ya zuwa karshen watan Mayu da ya wuce, yawan masana'antu da 'yan kasuwa na Hong Kong suka zuba musu kudin jari ya wuce 13,200 a Shenzhen, yawan kudin jari da suka zuba ya zarce dalar Amurka biliyan 42, wato ke nan ya dauki kashi sama da 60 cikin dari bisa jimlar kudin jari da 'yan kasuwa na kasashen waje suka zuba a birnin.

An ruwaito cewa, sama da kashi 70 cikin dari na masana'antu da Hong Kong ya kafa a birnin Shenzhen masana'antu ne da 'yan kasuwa na Hong Kong suka zuba musu kudin jari gaba daya, sa'an nan yawan kudin jari da suke zubawa shi ma yana ta karuwa. Haka kuma a cikin shekarun nan hudu da suka wuce, 'yan kasuwa na Hong Kong suna kara fadada fannonin tattalin arziki da suke zuba musu kudin jari a birnin wadanda suka hada da kere-kere, da jigilar kayayyaki, da sayar da kayayyaki, da harkokin kudi, da gidaje da al'adu da sauransu. (Halilu)