Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-27 07:36:35    
Kasar Sin ta yi koyi da kasar Japan wajen fasahar wasan kwallon gora

cri

Masu sauraro,kamar yadda kuka sani,kasar Sin da kasar Japan kasashe biyu ne mafiya karfi wajen wasannin motsa jiki a nahiyar Asiya,a kullum wadannan kasashe biyu suna yin takara mai sada zumunci a fannin wasannin motsa jiki.A sa`i daya kuma,kasashen nan biyu suna yin cudanya da kuma taimakon juna kan wannan cikin dogon lokaci.Alal misali,malamin wasa na kasar Japan Hirobumi Daimatu ya taba koyar da wasan kwallon boli na mata a kasar Sin,malamar wasa ta kasar Japan Masayo Imura tana koyar da wasan salon iyo na mata a kasar Sin,ana iya cewa,kasar Japan ta ba da amfaninta wajen ciyar da wadannan wasanni gaba a kasar Sin.Amma,a sa`i daya kuma,kasar Sin ita ma ta ba da gudumuwarta ga kasar Japan wajen bunkasa wasan kwallon tebur da wasan karate da sauransu.

Kila ba a taba gaya muku ba cewa,a cikin `yan shekarun da suka shude,kungiyar wasan kwallon gora ta kasar Japan tana yin kokari tana taimakawa `yan wasan kwallon gora na kasar Sin ta yadda kuma za a daga matsayin wasan kwallon gora na kasar Sin.A cikin shirinmu na yau,bari mu yi muku bayani kan wannan.

Daga shekarar 2002,kasar Sin ta fara shirya hadaddiyar gasar wasan kwallon gora ta sana`a,saboda an fara wasan kwallon gora ba dadewa ba a kasar Sin,kuma `yan wasan ba su da yawa,shi ya sa matsayin wasan na kungiyar kasar Sin yana baya baya,wato bai kai na kungiyar kasar Japan da na kungiyar kasar Korea ta kudu da kuma na kungiyar Taibei na kasar Sin ba.Daga baya,bayan kokarin da kungiyar kasar Sin ta yi,ta taba lashe kungiyar kasar Korea ta kudu a gun zama na 23 na gasar cin kofin Asiya ta wasan kwallon gora da aka shirya a shekarar 2005,ta zama lambatiri a Asiya,wannan shi ne sakamako mafi kyau da kungiyar kasar Sin ta samu a tarihinta.

Amma a kasar Japan,mutanen kasar suna kishin wannan wasa sosai,ana iya cewa kwallon gora shi ne kwallon kasa na kasar Japan.Kuma hadaddiyar gasar wasan kwallon gora na sana`a ta kasar tana da dogon tarihi,har ya riga ya kai shekaru fiye da 70.A gun gasar shahararrun kungiyoyin `yan wasan kwallon gora ta duniya da aka shirya bisa karo na farko a shekarar 2006,kungiyar kasar Japan ta zama zakara.Wannan gasa ita ce gasar kwallon gora mafi koli a duniya.

Don daga matsayin wasan kwallon gora,kasar Sin ta nuna kwazo da himma ta yi koyi da kasar Japan kan wannan,kasar Japan kuwa ita ma ta nuna goyon baya mai karfi ga kasar Sin wajen fasaha da kudi.

Kungiyar wasan kwallon gora ta damisa ta birnin Tianjing ta kasar Sin ita ce daya daga cikin kungiyoyi mafiya karfi a kasar Sin,don kyautata fasahar wasa,ta gayyaci malamin wasa Kosuke Matsuoka daga kasar Japan da ya koyar da `yan wasanta.Game da wannan,babban malamin wasa na kungiyar Jiao Yi ya ce :  `Ina ganin cewa `yan wasan kungiyata suna iya koyin sabuwar fasaha daga wajen malamin wasan kasar Japan,kodayake idan ana so a samu ci gaba a bayyane,dole ne a kashe lokaci da yawa.`

Malamin wasa Jiao Yi yana fatan za a ci gaba da yin irin wannan cudanya da hadin gwiwa.Ya ce :  `Ya fi kyau a ci gaba da gudanar da irin wannan huldar aiki saboda matsayin wasan kwallon gora na kasar Sin yana baya baya.`

Ban da wannan kuma,kamfanonin kasar Japan su ma sun ba da taimakon kudi ga hadaddiyar gasar wasan kwallon gora ta kasar Sin.Kazalika,wajen yadda ake tafiyar da harkokin hadaddiyar gasa,kamfanin shirya gasar wasan kwallon gora na kasar Sin wanda ke karkashin jagorancin kamfanin `soft bank` na kasar Japan yana shan ayyuka a fannoni daban daban,alal misali aikin yin farfaganda kan hadaddiyar gasa da aikin shirya hadaddiyar gasa da aikin yin cudanya da masu sha`awar kwallon gora da dai sauransu.

Shugaban hukumar kula da harkokin kungiyar wasan kwallon gora ta sana`a ta kasar Japan Kazuo Hasegawa ya bayyana cewa,  `A halin da ake ciki yanzu,abu mafi muhimmanci shi ne a kafa huldar hadin gwiwa wajen fasaha tsakanin kungiyoyin wasan kwallon gora na kasashen nan biyu wato kasar Sin da kasar Japan,bayan taron wasannin Olimpic na shekarar 2008 kuwa,za mu fara yin hadin gwiwa daga dukkan fannoni tsakaninmu.`

To,jama`a masu sauraro,karshen shirinmu na yau ke nan,ni Jamila da na gabatar nake cewa,ku zama lafiya,sai makon gobe war haka idan Allah ya kai mu.(Jamila Zhou)