Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-27 07:35:05    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (20/06-26/06)

cri

Ran 24 ga wata,aka kammala budaddiyar gasar kwallon tebur ta kasar Japan ta shekarar 2007,a gun gasar nan,kungiyar `yan wasan kasar Sin ta samu cikakkiyar nasara wato ta samu dukkan lambobin zinariya hudu.`Dan wasa daga kasar Sin Wang Hao ya zama zakaran maza,`Yar wasa daga kasar Sin Wang Nan ta zama zakarar mata.A gun gasar dake tsakanin maza biyu biyu,`yan wasa daga kasar Sin Wang Liqing da Chen Qi sun zama zakaru,a gun gasar dake tsakanin mata biyu biyu,`yan wasa daga kasar Sin Li Xiaoxia da Guo Yue sun zama zakaru.

Ran 24 ga wata,aka kammala gasa ta tashar kasar Jamus ta gasar ba da babbar kyauta ta wasan tsinduma cikin ruwa da hadaddiyar kungiyar wasan iyo ta kasashen duniya ta shirya a shekarar 2007.A gun gasa ta rana ta karshe,`yan wasa daga kasar Sin sun samu dukkan lambobin zinariya uku na wannan rana,wanda a ciki,Lin Yue ya zama zakaran maza na wasan tsinduma cikin ruwa daga kan dandamali mai tsayin mita goma,Wang Feng da He Chong sun zama zakarun gasar dake tsakanin maza biyu biyu ta wasan tsinduma cikin ruwa daga kan dandamali mai tsayin mita uku,ban da wannan kuma,Guo Jingjing da Wu Minxia sun zama zakarun gasar dake tsakanin mata biyu biyu ta wasan tsinduma cikin ruwa daga kan dandamali mai tsayin mita uku.Daga nan kungiyar kasar Sin ta samu zakarun wasanni takwas na wannan gasa.

Ran 23 ga wata,kungiyar wasan kwallon kafa ta Olimpic ta kasar Sin ta sauka a birnin Johannesburg bisa gayyatar kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Afrika ta kudu ta yi mata don hallartar gasar wasan kwallon kafa da za a shirya bisa gayyata tsakanin kasashe takwas a mako mai zuwa,a gun wannan gasa,ban da kungiyar kasar Sin,sauran kungiyoyi bakwai sun zo ne daga kasashen Afirka.Bisa shirin da aka tsara,kungiyar Olimpic ta kasar Sin za ta yi gasa da kungiyar kasar Airka ta kudu a ran 27 ga wata.(Jamila zhou)