Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-26 21:26:12    
Babban dutsen Xiangbishan da kuma kololuwar Duxiufeng

cri

Dukkan babban dutsen Xiangbishan da kuma kololuwar Duxiufeng suna cikin birnin Guilin na jihar kabilar Zhuang ta Guangxi mai tafiyar da harkokinta da kanta. Ma'anar Xiangbi a bakin Sinawa ita ce hancin giwa, 'shan' kuma shi ne babban dutse. Babban dutsen Xiangbishan ya kasance a wurin da kogin Yangjiang da kogin Lijiang suka hadu da juna. Siffar wannan babban dutse ta yi kama da yadda wata giwa ta sa babban hancinta a cikin kogin don debo ruwa. Akwai wata almara game da asalin babban dutsen Xiangbishan. A gaskiya kuma wannan babban dutse shi ne wata giwa da sarkin Aljanna ke mallaka. A yayin da wannan sarki ya nemi mamaye duniya, ya tilasta wa wannan giwa ta yi aikin sufuri tukuru, har ma wannan giwa ta kamu da ciwo, amma wasu manoma sun cece ta. Shi ya sa wannan giwa ta yi musu godiya, ta tsai da kudurin ci gaba da zama a duniya, tana son bai wa wadannan manoma taimako. Duk da haka sarkin Aljanna ya yi hushi saboda wannan giwa ta sanya babban hancinta a cikin kogin ta sha ruwa. Ta haka ya harba takobi ya sare ta, takobin ya sare ta a kan babban hancinta a cikin ruwan, wannan giwa ta zama babban dutsen da muke gani a yau. An gina wata rumfa a kan babban dutsen, wadda ta zama alamar takobin da sarkin Aljanna ya sara.

Kololuwar Duxiufeng tana daidai ne a tsakiyar birnin Guilin. Kyanta ya cancanci sunanta sosai, ma'anar Duxiu a Sinance ita ce kyakkyawar kololuwa daya tak a duniya. Kololuwar nan ta kasance mai launin shuni ko na zinariya a cikin hazo da sassafe ko kuma a cikin haske a lokacin faduwar rana. Bayan da masu yawon shakatawa suka kammala hawan benaye 306 sun isa kololuwar, sai a ba su wata lambar kyauta, wato suna iya hangen duk birnin Guilin daga nesa, haka kuma, suna iya ganin cewa, tsaunukan da ke kewayen kololuwar Duxiufeng sun yi kama da manyan kananan gorori. Kazalika kuma, masu yawon shakatawa sun iya kallon kogin Lijiang mai kwane-kwane da ke gangara a tsakanin wadannan tsaunuka, yana kuma gudu zuwa nesa.