Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-26 21:21:28    
Gidan ibada na Fayuansi, wani gidan ibada mai tsawon shekaru dubu da ke birnin Beijing

cri

A cikin birnin Beijing mai wadata, akwai wani gidan ibada mai tsawon shekaru dubu, sunansa shi ne gidan ibada na Fayuansi, shi ne kuma gidan ibada mafi dadewa da aka adana shi a nan Beijing. Cibiyar nazarin ilmin addinin Buddha ta kasar Sin ta mayar da wannan gidan ibada a matsayin babban zaurensa. A kan shirya wani gaggarumin bikin rubutattun wakoki a nan a ko wace shekara, mawallafa na kasar Sin da masu yawon shakatawa da yawa na gida da na waje suna alla-alla wajen halartar wannan biki. Yau ma bari mu kai ziyara ga wannan gidan ibada tare.

Gidan ibada na Fayuansi na cikin gundumar Xuanwu da ke kudancin birnin Beijing, fadinsa ya kai misalin murabba'in mita 6700. Saboda wani sarki na zamanin daular Tang ne ya ba da umurnin gina shi yau da shekaru fiye da 1300 da suka wuce, shi ya sa dukan tsarin ginin ya yi kama da fadar sarki na zamanin da. Bayan da aka yi kwaskwarima a kansa sau da dama, gine-ginen da ke cikin gidan ibada na Fayuansi da muke gani a yau gine-gine ne da aka gina a zamanin daular Ming da ta Qing wato daruruwan shekaru da suka wuce. Malam Yao Yuan, wanda ke aiki a cikin gidan ibada na Fayuansi, yana himmantuwa wajen nazarin tarihin gidan ibadan nan, ya kuma wallafi littattafan da abin ya shafa, ya yi karin bayanin cewa, 'Gidan ibada na Fayuansi wani gidan ibada ne mai dogon tarihi, wanda aka fara gina shi a zamanin daular Tang wato yau da shekaru fiye da 1300 da suka shige. Akwai labarun al'adu da tarihi da yawa game da shi. Yana da cikakken tsarin gini, fadinsa kuma ya yi girma. Sigar musamman tasa ita ce yana da dogon tarihi da kuma kyawawan al'adu.'

A cikin gidan ibada na Fayuansi, babban zauren Dabeitan wuri ne don nuna kayayyakin gargajiya, inda aka ajiye mutum-mutumin Buddha na dauloli daban daban na kasar Sin da kuma sauran kayayyakin fasaha masu daraja, ciki har da mutum-mutumin Buddha mafi tsoho na kasar Sin, wato mutum-mutumin Buddha da aka sassaka da tukwane a zamanin daular Donghan wato yau da shekaru fiye da 1900 da suka zarce. Ban da wannan kuma, an ajiye mutum-mutumin tagulla na Kwan-yin wato the Buddhist Goddess of Mercy a babban zauren Guangyindian. Tsayinsa ya kai santimita 50 ko fiye, an nuna nagartacciyar fasaha wajen sassaka shi yadda ya kamata. Abu mai ban mamaki shi ne digo-digon ruwa suna ta fitowa a cikin hannayen wannan mutum-mutumin tagulla, har zuwa yanzu ba a san dalilin da ya sa haka ba tukuna. An yi karin bayani cewa, masu bin addinin Buddha da masu yawon shakatawa da yawa daga kasashen waje sun je kallon wannan mutum-mutumin tagulla na Kwan-yin saboda kyakkyawar sifarsa da mamakinsa.

Ba kawai wuri ma tsarki a cikin addinin Buddha ba, gidan ibada na Fayuansi wani wurin yawon shakatawa ne da ke nasaba da harkokin al'adu sosai. Bikin rubutattun wakoki da a kan shirya domin jin dadin ganin furannin clove a watan Afril na ko wace shekara ya sami karbuwa a cikin masu yawon shakatawa. An riga an yi shekaru 80 ko fiye ana shirya wannan biki.Furannin clove ire-ire da yawa suna girma sosai a gidan ibada na Fayuansi. Launukansu sun sha bamban da juna, ban da furen clove mai launin fari da mai ruwan hoda iri na kasar Sin, akwai wani irin furen clove da aka kawo shi daga tsibirin Maluku na kasar Indonesia yau da shekaru fiye da dai 6 da suka shige.

A ko wace rana da karfe 3 da rabi da yamma, 'yan addinin Buddha sun fara karanta littattafan addini a gidan ibada na Fayuansi. Ban da wasu 'yan addinin Buddha da ke zama a gidan ibadan nan, 'yan addinin Buddha dalibai fiye da 100 na kwalejin ilmin addinin Buddha na kasar Sin suna karatu a nan. Malam Fan Hua, wani dan addinin Buddha a nan, ya taba karatu a cikin kwalejin ilmin addinin Buddha na kasar Sin. Ya ji ya taki sa'a saboda ya sami damar koyon addinin Buddha a wadannan wurare 2, ya ce, 'Gidan ibada na Fayuansi ya sha bamban da saura, yana da harsashin al'adu mai inganci. Mu 'yan addinin Buddha mun ji alfahari sosai domin zama a nan. A ko wace rana muna bin ka'idojin da aka tsara yau da shekaru dubu daya ko fiye. Muna karatu da zama a cikin irin wannan wuri ta hanyar da magabatanmu suka bi. Wannan shi ne dama mai kyau da muka samu, haka kuma masu bin addinin suna alla-alla wajen zuwa nan. Shi ya sa muke sakin jiki a nan.'

Malama Carla Prevato, 'yar kasar Italiya ta kawo wa gidan ibada na Fayuansi ziyara tare da iyalinta a karo na farko, sun kuma shiga bikin rubutattun wakoki. Ta gaya mana cewa, 'A can da ba mu san wannan gidan ibada ba, kaddara ce mun kawo nan ziyara. Gidan ibadan nan na da kyan gani sosai, mun ji sakin jiki da kwanciyar hankali a nan.'