Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-25 18:37:30    
Ana daukar matakan musamman wajen shawo kan cututtuka masu tsanani a lardin Qinghai

cri

Li Maocaidan, wani manomi ne na kauyen Awubuju na gundumar Hulong ta kabilar Hui mai cin gashin kai da ke lardin Qinghai na kasar Sin. Sabo da faman da yake da talauci, shi ya sa ko da yake ya kamu da cutar tarin huka wato tibi, amma ba shi da kudin ganin likita. A 'yan kwanakin nan da suka gabata, wani asibitin wurin ya warkar da shi ba tare da karbar ko wane kabo ba, shi ya sa Li Maocaidan ya sake iya yin aikin noma a gonakinsa. Kuma ya gaya mana cewa, "lokacin da nake fama da cutar tibi, ban iya yin numfashi kamar yadda ya kamata, lokacin da nake yawo, balle ma na yi noma. Abin mamaki shi ne gwamnatin wurinmu ta samar da kudi wajen warkar da ni. Yanzu na sake samun karfin yin noma a gonakina. Haka kuma zan iya fita waje domin cin rani a nan gaba kamar yadda sauran 'yan kauyenmu suke yi."

Cutar tibi wata cuta ce mai tsanani da ke iya harbar mutane, haka kuma tana daya daga cikin muhimman cututtukan da ke iya haddasawa manoma da makiyaya su fada cikin talauci sakamakon cututtuka. A cikin shekaru fiye da goma da suka gabata, yawan mutanen da ke fama da cutar tibi a duk duniya ya sake samun karuwa sosai. A shekara ta 2001, gwamnatin lardin Qinghai ta tsara tsarin shawo kan cutar tibi na lardin Qinghai, inda aka tsai da kudurin cewa, daga shekara ta 2002, za a dauki matakai a jere wajen warkar da mutanen da suke fama da cutar tibi da sauran cututtuka ba tare da karbar kudi ba a duk fadin lardin. Kuma ya zuwa yanzu an riga an warkar da mutane masu dimbin yawa kamar Li Maocaidan da muka ambata a baya.

Ma Yongcheng, shugaban sashen shawo kan cutar tibi na cibiyar shawo kan cututtuka ta lardin Qinghai ya gaya wa wakilinmu cewa, "yanzu ana gudanar da aikin shawo kan cutar tibi a dukkan birane da gundumomi na lardin Qinghai, ciki har da mutanen da ke sanya wuraren zama. A 'yan shekarun nan da suka gabata, ta hanyar yin binciken lafiya ba tare da karbar kudi ba, an gano mutanen da aka tuhumar kamuwa da cutar tibi kusan dubu 100, haka kuma yawan mutane masu fama da cutar da aka warkar da su ya kai fiye da dubu 10, wato yawan mutanen da ake zargin cewa su kamu da cutar tibi ya kai kashi 73 cikin dari, kuma yawan mutanen da aka warkar da su ya kai kashi 90.5 cikin dari. Sabo da haka an hana yaduwar cutar tibi sosai, kuma an biya bukatar tsarin shawo kan cutar tibi na lardin Qinghai na wannan mataki. "

A hakika dai, sarrafa da kuma shawo kan cutar tibi yana daya daga cikin matakan musamman da lardin Qinghai ke dauka wajen shawo kan cututtuka masu tsanani. Sabo da ana iya samun cututtuka masu yaduwa iri daban daban a lardin Qinghai, shi ya sa daga shekara ta 2001, aka fara daukar matakan musamman masu yawa wajen shawo kan cututtuka a duk fadin lardin, ciki har da ciwon ciki mai yaduwa da ciwon rashin sinadarin iodine da ciwon kanjamau da dai sauransu.

Game da cutar kanjamau, gwamnatin lardin Qinghai ta dauki matakai wajen shawo kan cutar, ciki har da yin jiyya ga mutane masu fama da talauci da suke fama da cutar kanjamau ba tare da karbar kudi ba, da gudanar da binciken lafiya ga mutanen da suke fama da cutar bisa son ransu, da yin jiyya ga matan da ke da ciki kuma suna fama da cutar ba tare da karbar kudi ba a unguwar gwaji ta shawo kan cutar kanjamau, da sa yaran da iyayensu suka mutu sakamakon cutar kanjamau su shiga makaranta ba tare da karbar ko kwabo ba, da tallafa wa mutanen da suke fama da cutar kanjamau wajen zaman rayuwarsu.

Bayan da aka dauki matakan musamman wajen shawo kan cututtuka masu tsanani, yawan mutanen da suka kamu da cututtuka masu yaduwa iri daban daban a lardin Qinghai ya samu raguwa sosai. Jie Xuehui, mataimakin shugaban ofishin kiwon lafiya na lardin Qinghai ya bayyana cewa, a shekarar da muke ciki, hukumar kiwon lafiya ta lardin za ta kara kebe kudi domin ci gaba da kyautata matakan musamman wajen shawo kan cututtuka masu tsanani. Kuma ya kara da cewa, "A shekarar nan, gwamnatin lardin Qinghai ta tsai da kudurin sake kebe kudaden da yawansu ya kai kudin Sin Yuan miliyan 140 domin ci gaba da tafiyar da abubuwa goma masu amfana wa fararen hula manoma da makiyayya. Kuma na yi imanin cewa, bisa kokarin da ake yi, za a iya shawo kan cututtukan da a kan samu a Plateau da kuma wasu wurare sosai a lardin Qinghai." Kande Gao)